An Shiga Rudani Yayin Da Matasa Suka Farmaki Cocin RCCG, Sun Lalata Kayayyaki Da Dama
- Wasu fusatattun matasa sun yi ɓarna a cocin RCCG ana cikin gudanar da Ibada
- Matasan da suka ƙunshi maza da mata, sun lalata kayayyaki irinsu kujeru da gangunan cocin
- Bidiyon ta'asar da suka yi ya yaɗu a shafukan sada zumunta inda jama'a suka tofa albarkacin bakunansu
Wasu matasa da ba a iya tantance ko su waye ba, sun farmaki cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), inda suka hargitsa ta ana cikin gudanar da Ibada.
An ɗora bidiyon a shafin Curthbet Chinedu na TikTok, wanda ke nuna lokacin da matasan maza da mata ke tada hargitsi gami da lalata kayayyakin cocin.
Yadda matasa suka farmaki cocin RCCG
Duk da dai ba a iya tantance ko a wane wuri ba ne lamarin ya faru, Legit.ng ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ɗaya daga majami'o'in Fasto Enoch Adejare Adeboye.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cikin bidiyon za a iya ganin yadda matasan suka lalata kujeru da gangunan cocin, kafin daga bisani kuma suka tunkari faston da ke jagorantar Ibada a lokacin.
Faston ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya tsayar da su daga abinda suke aikatawa, sai dai dole ya haƙura daga ƙarshe ya sanyawa sarautar Allah ido.
Kalli bidiyon a nan ƙasa:
Martanin mutane kan hargitsin cocin RCCG
Masu amfani da kafar TikTok da dama sun tofa albarkacin bakunansu biyo bayan wallafar bidiyon hargitsin da aka samu a cocin RCCG kamar haka:
johnnyrich64 ya ce:
“Mai ɗaukar bidiyo !!! Na yafe ma ka saboda coci ka tsaya ka yi bidiyo. Amma idan a gaba ka ƙara ɗora bidiyo ba tare da bayani ba za ka ga abinda zan yi ma ka.”
God's Favourite ya ce:
“Wannan abin baƙin ciki ne. Ya mutum zai yi haka a ɗakin Ubangiji.”
stanlo ya ce:
“Komai yana tafiya lafiya lau har zuwa lokacin da faston ya faɗi wata magana mara tsari.”
'Yan bindiga sun yi garkuwa da malaman coci 2 a Neja
Legit.ng a baya ta kawo mu ku wani rahoto kan garkuwa da wasu malaman coci biyu da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a farko-farkon watan Agustan da muke ciki, inda masu garkuwa da mutanen suka je har gida suka yi awon gaba da malaman cocin.
Asali: Legit.ng