Juyin Mulki: Atiku Ya Shawarci ECOWAS Da AU Da Su Yi Kokarin Mayar Da Sojoji Zuwa Bariki

Juyin Mulki: Atiku Ya Shawarci ECOWAS Da AU Da Su Yi Kokarin Mayar Da Sojoji Zuwa Bariki

  • Dan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi martani kan juyin mulkin Gabon
  • Atiku ya yi Allah wadai da hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo da sojojin ƙasar Gabon suka yi ranar Laraba
  • Ya shawarci ECOWAS da AU da su hau kan teburi da sojojin juyin mulki domin tabbatar da dimokuraɗiyya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da kifar da gwamnatin Ali Bongo na ƙasar Gabon da sojoji suka yi.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.

Atiku Abubakar ya bai wa ECOWAS da AU muhimmiyar shawara
Atiku ya shawarci ECOWAS da AU da su yi ƙoƙarin mayar da sojoji zuwa barikokinsu. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku ya shawarci ECOWAS, AU su tattauna da sojoji

Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne a lokacin Obasanjo, ya bukaci ECOWAS da Tarayyar Afrika (AU), da su tattauna da sojojin juyin mulki cikin lumana domin ganin sun koma bariki.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Laraba 30 ga watan Agusta ne dai aka wayi gari da sanarwar kifar da gwamnatin Ali Bongo na Gabon da sojojin ƙasar suka yi.

Atiku da ya ke martani a kan lamarin, ya ce dimokuraɗiyya tana nan daram dam, kuma ya zama wajibi a yi duk abinda ya kamata wajen ci gaba da tabbatuwarta.

Atiku ya kuma koka kan yadda aka samu juyin mulki a ƙasashe takwas cikin abinda bai wuce shekaru uku ba, inda ya ce akwai bukatar a yi nazari kan abinda ke janyo hakan.

Sojojin Najeriya sun fara ɗaukar mataki bayan juyin mulki

A baya Legit.ng ta yi wani rahoto kan wani mataki na rigakafi da ake ganin rundunar sojin Najeriya ta fara ɗauka dangane da juyin mulkin da ake samu a ƙasashen Afrika.

Kara karanta wannan

Kungiyar Musulunci Ta Aike Da Sako Mai Muhimmanci Ga Sojojin Najeriya Kan Juyin Mulkin Gabon

Kwamandan runduna ta 81 ta sojin Najeriya, Mohammed Takuti Usman a yayin da yake jawabi ga sojojin yaki a Abeokuta ta jihar Ogun, ya bukaci su kasance masu biyayya ga shugaban ƙasa da sauran shugabanni.

Haka na zuwa ne jim kaɗan bayan kifar da gwamnatin farar hula a ƙasar Gabon da sojoji suka yi.

Ali Bongo ya nemi ƙasashen duniya su kawo ma sa ɗauki

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan buƙatar da hamɓararren shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo ya miƙa cikin wani faifan bidiyo, inda ya nemi ƙasashen duniya su kawo ma sa ɗauki.

Bongo ya koka kan yadda ya ce sojojin juyin mulkin sun ajiye shi a wani waje daban da inda suka ajiye iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng