Jami’in Dan Sanda a Adamawa Ya Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Sallame Shi a Aiki, Bidiyon Ya Yadu

Jami’in Dan Sanda a Adamawa Ya Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Sallame Shi a Aiki, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya sannan ya haddasa cece-kuce yayin da wani jami'in dan sanda ke kuka da hawaye kan sallamarsa da aka yi a aiki
  • Rundunar yan sandan Adamawa ta tsige wasu jami'anta biyu Ahmed Suleiman da PC Mahmood Muhammed kan bata suna da aikata ba daidai ba
  • An gurfanar da jami'an tsaron a dakin shari'a sannan rundunar ta kama su da aikata laifin da ake tuhumarsu a kai tare da yanke hukuncin sallamarsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Adamawa - Wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, ya nuno lokacin da wani jami'in dan sanda ke sharban kuka wiwi bayan an sallame shi daga aiki saboda ya aikata ba daidai ba.

An sallami wasu jami'an yan sanda a Adamawa
Jami’in Dan Sandan Adamawa Ya Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Sallame Shi a Aiki, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Rundunar yan sandan jihar Adamawa, ta gurfanar da wasu jami'anta biyu, Inspekta Ahmed Suleiman da PC Mahmood Muhammed wanda ke aiki da hedkwatar rundunar ta Dumne a dakin shari'a.

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

An gurfanar da jami'an kan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da bata suna, kisan kai, da kuma gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba, rahoton The Punch.

Rundunar ta same su da laifi kan tuhumar da ake masu sannan ta ba da shawarar korar dukka masu laifin, za a gurfanar da su dukka biyun a gaban kotu tare da sauran wadanda ake zargi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tubewa dan sandan mai karamin matsayi kayan aiki yayin da za a cirewa sufeton nasa bayan ya cika wasu ka'idoji.

Sallama: Yan Najeriya sun yi martani yayin da jami'in dan sanda ke kuka kamar karamin yaro

Kamar yadda aka saba bisa al'ada, yan Najeriya da dama sun garzaya sashin sharhi a manhajar X domin bayyana ra'ayinsu a kan bidiyon.

@TheFelix__ ya yi martani:

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Tsere Daga Dazuzzuka, Sun Saki Wadanda Suka Sace a Arewa

"Duk da wannan, ba za su koyi darasi ba."

@Hamsuf ya yi martani:

"Mutumin da zai fara kiran wannan gayen da "ofisa" sannan ya yi dariya ne nake tausayawa."

@omobenintv ya ce:

"Yallabai a tafi gida."

@LateefK50823714 ya ce:

"Wannan ne hukunci mai kyau da ya kamata a dunga yi wa jami'an yan sanda da suka aikata ba daidai ba."

Kalli bidiyon a kasa:

MURIC ta gargadi sojojin Najeriya bayan juyin mulkin Gabon

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta shawarci rundunar sojojin Najeriya da kada ta yi koyi da sojojin Gabon da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo a ranar Laraba.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayar da shawarar a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng