Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Ogun Sun Duka Domin Neman Afuwa a Gaban Gwamna Abiodun
- Shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ogun sun ɗuka a gaban gwamna Dapo Abiodun bayan ɗaya daga cikinsu ya kai ƙorafin gwamnan
- Wale Adedayo, shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas, ya zargi gwamnan da riƙe kason ƙananan hukumomin har na shekara biyu
- A cikin ƙorafin, Adebayo ya buƙaci tsohon gwamnan jihar Segun Osoba da ya sanya baki kan lamarin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abeokuta, jijar Ogun - Jihar Ogun ta tsinci kanta a cikin wata dirama a ranar Talata, 29 ga watan Agusta, lokacin da shugabannin ƙananan hukumomin jihar suka duƙa a gaban gwamna Dapo Abiodun.
Shugabannin ƙananan hukumomin sun duƙa a gaban gwamnan ne domin ya yafe musu bayan ɗaya daga cikinsu ya rubuta ƙorafi a kansa.
An zargi Abiodun da wawurar kuɗaɗe
A cikin wasiƙar ƙorafin, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Wale Adebayo, shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas, ya yi zargin cewa gwamnan ya riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin ƙorafin na sa, Adebayo ya koka kan cewa shugabannin ƙananan hukumomi a jihar, sun kasa gudunar da ayyuka a cikin shekara biyun da suka gabata.
Adebayo ya yi kira ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su binciki gwamna Abiodun kan karkatar da kuɗaden ƙananan hukumomin.
A cewar Adebayo, gwamnan ya ƙi ya ba su ko sisi daga cikin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya take bayarwa a shekara biyu da suka gabata.
Dalilin dukawar shugabannin a gaban Abiodun
Shugabannin ƙananan hukumomin a ƙarƙashin jagorancin, Emilola Ghazal, shugaban ƙaramar hukumar Ijebu-Ode sun nemi afuwa a wajen gwamnan.
A yayin neman afuwar ta su, shugabannin ƙananan hukumomin sun nuna takaicinsu kan abin da Wale ya yi, inda suka ɗuka ƙasa kan gwiwoyinsu domin nuna cewa sun tuba.
APC Ta Yi Amai Ta Lashe
A wani labarin kuma, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amai ta lashe kan jerin sunayen ƴan tawagar yaƙin neman zaɓenta a zaɓen gwamnonin jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.
Jam'iyyar ta bayyana cewa sunayen da ke yawo na ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen ba daga gareta suka fito ba.
Asali: Legit.ng