Wani Dan Najeriya Ya Fallasa Tulin Zinare Da Ke Wani Kauye a Arewa, Ya Saki Hujjojin Bidiyo
- Wani dan Najeriya ya garzaya soshiyal midiya don fallasa wani wurin hakar zinare a jihar Zamfara
- A cewar mutumin, wurin hakar zinaren haramtacce ne kuma mallakin wani sanata mai ci, tsohon soja kuma tsohon gwamna ne
- Jama'a sun yi martani kan bidiyon wajen hakar zinare yayin da mutane suka yi Allah wadai da hakan tare da caccakar gwamnati
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Mahdi Shehu, mai sharhi kan al'amuran jama'a ya fallasa wani haramtaccen wurin hakar zinare a wani kauye a jihar Zamfara.
Mai rajjin kare hakkin dan adam din ya kuma saki wani faifan bidiyo da ke nuna ma'aikatan da ke aikin hakar zinare a yayin da ya yi karin haske kan mamalakinsa.
Shehu ya yi ikirarin cewa wani tsohon gwamna ne ke da wurin
A cewar Shehu, harataccen wurin hakar zinaren mallakin wani tsohon soja mai ritaya, tsohon gwamna kuma sanata mai ci ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewar ana biyan laburori Naira 1000 a kullun kuma ya yi mamakin yadda ba a samu matsalar yin garkuwa da mutane a wurin ba.
Ya rubuta:
"HARAMTACCEN WURIN HAKAR ZINAREN ZAMFARA: Wurin yana a karamar hukumar Anka. Wajen mallakin wani tsohon gwamna, Janar mai ritaya kuma sanata mai ci ne. Ashe shiyasa ba a taba garkuwa da mutane a wuraren hakar ma'adinai saboda suna da kariya sosai. N1000 duk kwanan duniya ga kowane ma'aikaci. Wata runduna?"
Shehu ya yi karin haske kan haramtaccen wurin hakar zinarin
Dan fafatukar ya yi zargin cewa wajen hakar ma'adinan kamar fasa bututun mai ne, wanda ke samun goyon bayan masu hannu da shuni tare da kariya daga guggun miyagu a kudu.
Legit.ng ba za ta iya tabbatar da wannan ikirari na Shehu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani kan haramtaccen wajen hakar zinare a Zamfara
@fouta_djallon ya ce:
"A matsayina na masanin kimiyyar ma'adinai, tawagata na yawan ziyartar wannan wuri shekaru da yawa da suka wuce. Tulin zinaren na iya ciyar da Arewa har tsawon shekaru 100 idan aka kula da shi sosai amma me na sani?"
@Landlordoflagos ya ce:
"Najeriya kamar daji ce.
"Idan mutum ya samu masaniya kan abun da mutane ke fitarwa daga kasar nan a kullun, mutum zai sha mamaki."
@DeborahToluwase ta ce:
"Ina ma ace za mu samu ministan ma'adinai mai tasiri wanda zai tayar da wannan batu. Zinaren da ke Zamfara idan aka hako su bisa ka;'ida zai janyo masu zuba hannun jari da sauransu cikin kasar nan."
Garin kwaki ya yi ajalin wata yarinya a Kano
A wani labari na daban, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a fadin kasar, ibtila'i ya afkawa wasu iyali a jihar Kano inda ake zargin garin kwaki ya yi ajalin wata yarinya tare da galabaita yan uwanta su biyar.
Jaridar Aminiya ta rahoto cewa yarinyar mai suna Firdausi Mahmud Abdullahi ta kwanta dama sakamakon cin garin kwaki da ta yibayan ta shafe tsawon lokaci ba tare da ta aka komai a cikinta ba.
Asali: Legit.ng