Ma'aikatan Kananan Hukumomin Jihar Plateau Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Ma'aikatan Kananan Hukumomin Jihar Plateau Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

  • Ma'aikatan ƙananan hukumomi a jihar Plateau sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a faɗin jihar
  • Ma'aikatan sun fara yajin aikin ne bisa tsoron rikicin da ka iya ɓarkewa a tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da PDP
  • Rikicin dai ka iya ɓarkewa ne a dalilin mayar da dakatattun shugabannin ƙananan hukumomin jihar kan muƙamansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Plateau - Mambobin ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi (NULGE) a jihar Plateau, sun shiga yajin aikin sai baba ta gani a faɗin jihar.

Mambobin sun tsunduma yajin aikin ne bisa abin da suka kira tsoron faɗan da ka iya ɓarkewa a tsakanin magoya bayan shugabannin ƙananan hukumomin da aka mayar kan muƙamansu, da shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin na jihar a ranar Litinin.

Ma'aikatan kananan hukumomin jihar Plateau sun shiga yajin aiki
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Yohana Makwin Arondon, wanda shi ne shugaban ƙungiyar shi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Sabbin Bayanai Kan Matsayar ECOWAS

Ƙungiyar dai ta yanke hukuncin tsunduma yajin aikin ne kwana ɗaya bayan kwamishinan ƴan sandan jihar ya mayar da shugabannin ƙananan hukumomi 17 da aka dakatar kan muƙamansu, da bayar da umarnin DPO na ƙananan hukumomin su yi musu jagora.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugabannin da aka mayar kan muƙaman na su dai waɗanda aka zaɓa ne a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, amma gwamnan jihar Caleb Mutfwang, ya dakatar da su bisa zargin yin watanda da dukiyar al'umma, zargin da suka musanta.

Dalilin shigar su yajin aiki

Sai dai, ma'aikatan ƙananan hukumomin sun bayyana cewa sun shiga yajin aikin ne domin rikicin da ka iya ɓarkewa a tsakanin magoya bayan APC da PDP a sakatariyoyin ƙananan hukumomin.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ba ta damu da damɓarwar siyasar da ke faruwa a tsakanin ɓangarorin biyu ba, abin da ya dame ta shi ne lafiyar mambobinta waɗanda komai na iya faruwa a kansu, saboda ba a san abin da zai faru ba.

Kara karanta wannan

Dalibin Ajin Karshe a Jami’a Ya Fadi Matacce Yan Kwanaki Kafin Rubuta Jarabawar Karshe

A kalamansa:

"Hakan ya sanya a matsayinmu na ƙungiya wacce albashin mambobinta shi ne mafi ƙaranci a jihar, ba za mu iya ɗaukar kasadar jefa rayukan mambobinmu cikin hatsari ba, hakan ya sanya muka yanke hukuncin kiran taron gaggawa a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, domin fara yajin aikin sai baba ta gani wanda zai fara daga ƙarfe 12:00 na dare har sai an warware rikicin."
"Wannan matakin ya zama wajibi ne domin kada rikicin ya ritsa da mambobinmu waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba."

Rabon Mukamai Ya Tada Kura a Plateau

A wani labarin kuma, rabon muƙaman kwamishinoni da gwamna Caleb Mutfwang ya yi a jihar Plateau ya bar baya da ƙura.

Gwamnan ya bayar da kaso 99% na kwamishinonin jihar ga Kiristoci, wanda hakan ya sanya aka yi ta sukar gwamnan ta kowane ɓangare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng