Najeriya Na Asarar Gangar Danyen Man Fetur 400,000 a Kowacce Rana, Nuhu Ribadu

Najeriya Na Asarar Gangar Danyen Man Fetur 400,000 a Kowacce Rana, Nuhu Ribadu

  • Babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya bayyana dalilin da ya sanya rayuwa ke ƙara tsada a Najeriya
  • Nuhu Ribadu ya bayyana cewa satar ɗanyen man fetur da ake yi a ƙasar nan shu ne dalilin da ya sanya rayuwa ta ƙara yin tsada a ƙasar nan
  • Ribadu ya bayyana cewa a kowacce rana ɓata-gari na satar ɗanyen mai ganga 400,000, wanda hakan ke janyowa ƙasar nan asarar miliyoyin kuɗi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Abia - Babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa har yanzu Najeriya tana asarar gangar ɗanyen man fetur 400,000 a kowace rana, a hannun ɓarayin man fetur na gida da wajen ƙasar nan.

Malam Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar da shugaban ƙasa ya wakilta zuwa duba wasu wurare na man fetur da iskar gas a yankunan Owaza na Jihar Abia da Odogwa na ƙaramar hukumar Etche a jihar Rivers, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

"Ba Zai Yiwu Ba": Sojojin Nijar Sun Bayyana Dalilin Kin Dawo Da Bazoum Kan Mulki

Nuhu Ribadu ya ce gangar mai 400,000 ake sacewa kullum a Najeriya
Nuhu Ribadu tare da yan tawagarsa Hoto: NNPCL
Asali: Twitter

Ribadu ya bayyana cewa satar ɗanyen man fetur ɗin ita ce babban dalilin da ya sanya ake fama da matsalar tsadar rayuwa a ƙasar nan.

Najeriya na tafka asara saboda satar ɗanyen mai

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Abin takaici ne yadda wasu mutane ƴan tsiraru su ke satar albarkatun ƙasarmu domin amfanar da kawunansu, abin da kuma ke haifar da asara mai yawa ga ƙasarmu da mutanen yankin."
"Najeriya za ta iya haƙo gangar man fetur miliyan biyu a kowacce rana, amma yanzu ƙasa da ganga miliyan 1.6 kawai muke iya haƙowa, saboda ayyukan ɓarayin man fetur da masu fasa bututun man fetur."
"Hakan na nufin kenan miyagu masu yi wa tattalin arzƙin ƙasa zagon ƙasa na sace gangar man fetur 400,000 kowacce rana domin amfanin kansu."
"Darajar gangar man fetur 400,000 a yanzu ta kai $4m, hakan na nufin a kowacce rana muna asarar waɗannan maƙudan kuɗaɗe a dalilin ayyukan ɓata gari.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Sabbin Bayanai Kan Matsayar ECOWAS

"Idan aka lissafa $4m sau 365, za ka ga cewa biliyoyin kuɗi masu yawa ƙasar nan ke asara a duk shekara."

Za a Siyar Da Gas Mai Arha

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa ƴan Najeriya albishir ɗin siyar da iskar gas mai arha a ƙasar nan, domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa za a riƙa siyar da iskar gas ɗin akan farashin N250 duk lita, inda ya buƙaci ƴan Najeriya da su mayar da ababen hawansu masu amfani da iskar gas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng