Dangote Ya Sake Zama Mutumin da Ya Fi Kowa Kudi a Afirka, Ya Tara Sama da $11Bn
- Aliko Dangote ya dawo da kambinsa a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka bayan da ya yi rasa matsayin ga hamshakin attajirin Afrika ta Kudu
- Adadin kudin Dangote a yanzu na kara haurawa duk da matsin karyewar darajar Naira a cikin kwanakin nan na baya
- Sauran hamshakan attajirai na Najeriya da ke kan gaba sun hada da Abdulsamad Rabiu da Mike Adenuga, kuma su ma suna ta habaka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote ya kara kwato matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika.
A cewar Forbes, dukiyar dan kasuwan na fannin masana'anta ta haura zuwa dala biliyan 11.2 a ranar Lahadi, 27 ga Agusta, 2023.
Wannan yana nuna karuwar 8.73% ko kuma dala miliyan 900 a dukiyar tasa idan aka kwatanta da dala biliyan 10.3 da ya mallaka a farkon watan Agusta.
Kididdigar attajirai ta Forbes
Karin dukiyar Dangote a yanzu ta cike gibin da ke tsakanisa da babban abokin hamayyarsa, hamshakin attajirin Afrika ta Kudu Johann Rupert.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Forbes, Rupert yana da kudi dala biliyan 10.2 ya zuwa ranar Lahadi 27 ga watan Agusta, wanda ya yi kasa da na Dangote da dala biliyan 1 da Dangote.
A farkon watan Agusta, Forbes ta ruwaito Rupert yana da mallakar kudin da suka kai dala biliyan 11.8.
A cikin kwanaki 23 da suka gabata, Rupert ya yi asarar sama da dala biliyan 1.1.
Tashin kudin Dangote nan da nan
Karuwar arzikin Dangote ya biyo bayan irin ribar da ya kwasa daga kamfanoninsa na kasuwanci a kasuwar musayar hannayen jari ta Najeriya, musamman kamfanonin simintinsa a makon jiya.
Binciken Legit.ng ya nuna cewa a cikin kwanaki 8 kacal arzikin Dangote ya karu da dala miliyan 200.
Karauniya Yayin Da Kotu Ta Daure Mutum 2 Kan Zargin Satar Kayan Motocin Dangote Na N976,715, Ta Yi Bayani
Dangote shi ne ya fi kowa hannun jari a kamfaninsa na siminti, kuma yawancin dukiyar da yake samu na fitowa ne daga yadda hannun jarin kamfanin ke habaka.
Bayanai daga NGX sun nuna cewa a ranar 17 ga watan Agusta, farashin hannun jari daya na simintin Dangote ya kai N349.9.
Ya zuwa sa'an karshe na kasuwa a ranar Juma’a, 25 ga watan Agusta, 2023, ya karu zuwa N360 kan kowanne hannu.
Arzikin sauran attajiran Najeriya
Baya ga Dangote, akwai manyan 'yan kasuwa a Najeriya da ke da tarin dukiya. Su ne kamar haka:
- Abdulsamad Rabiu - $6.1bn
- Mike Adenuga - $3.6bn
Jarin Dangote ya karye da $400m a baya
A wani labarin, Aliko Dangote dai ya sake samun koma baya a yawan kudinsa sakamakon faduwar darajar Naira, lamarin da ya rage darajar kadarorinsa da dukiyarsa na koma kasa da dala biliyan 11.
Arzikin attajirin na Najeriya ya ragu daga dala biliyan 11.2 a ranar 4 ga watan Agusta zuwa dala biliyan 10.8, ya samu faduwar dala miliyan 400 kenan a rana daya kacal a cewar Forbes.
A halin yanzu, a cikin jerin attajirai da aka sabunta a ranar 5 ga Agusta, 2023, Dangote ya koma matsayinsa na daya, inda dukiyarsa ta haura dala biliyan 13.5 ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Asali: Legit.ng