Sojin Nijar Sun Umarci Dakarunsu Da Tsayawa Cikin Shirin Ko Ta Kwana Don Yaki Da ECOWAS
- Sojin juyin mulki a Nijar sun umarci dakarunsu da tsayawa cikin shirin ko ta kwana don dakile harin bazata
- Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban tsaron kasar ya fitar a ranar Juma'a
- Wata majiyar ta ce an ba da umarnin ne don ankarar da sojin Nijar na tsayawa cikin shirin ko ta kwana
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yamai, Nijar - Sojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar sun umarci dakarunsu da su zauna cikin shiri yayin da su ke fuskantar barazanar yaki.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban tsaron kasar ya fitar a ranar Juma'a 25 ga watan Agusta.
Meye sanarwar sojin Nijar ke cewa?
An tabbatar da sahihancin bayanin yayin da aka yada ta kafar Intanet a yau Asabar 26 ga watan Agusta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Majiya daga jami'an tsaron kasar sun tabbatar da ingancin labarin, cewar Reuters.
Majiyar ta ce umarnin zai ankarar da sojin Nijar ne na tsayawa cikin shirin ko ta kwana yayin da ake tsammanin farmaki daga ECOWAS.
Har ila yau, hakan zai taimakawa sojin kasar don tunkarar duk wata barazana ta ba zata daga abokan gaba.
Majiyar ta ce:
"Akwai barazanar kawo hari a ko wane lokaci zuwa kasar."
Meye martanin ECOWAS kan Nijar?
Sai dai kungiyar ECOWAS ta bakin shugabanta, Alieu Touray a ranar Juma'a 25 ga watan Agusta ta ce ba su ayyana yaki ko shirin mamayar kasar Nijar ba.
Touray ya ce kungiyar ECOWAS za su bi duk wata hanya ko da karfin soja ne don dawo da mulkin dimukradiyya.
Ya kara da cewa Jamhuriyar Nijar a matsayinta na mamban ECOWAS na karkashin dokokin kungiyar na yaki da ta'addanci da kuma tabbatar da dimukradiyya.
A ranar 26 ga watan Yuli ne sojin kasar su ka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, cewar VOA.
Kungiyar ECOWAS ta ce za ta ba da duk wata dama na zaman teburi don sulhu tare da umartan dakarunta tsayawa kan shiri.
Ni Na Ke Hana ECOWAS Afkawa Nijar, Bola Tinubu
A wani labarin, shugaba Tinunu ya bayyana cewa ba don shi ba da tuni ECOWAS ta afkawa sojin Nijar.
Ya ce kawai ya na taka tsantsan ne kan shirin tura sojin ECOWAS zuwa Nijar da tuni mai afkuwa ta afku.
Asali: Legit.ng