Da Gaske Ne an Kori Jakadan Najeriya, Amurka da Jamus Daga Kasar Nijar? Gaskiya Ta Fito
- Rahoton da muke samu daga jamhuriyar Nijar na bayyana yadda kori jakadan kasar Faransa ba na sauran kasashe uku ba
- An yayata jita-jitan cewa, an kori jakadun kasashen Jamus, Amurka, Najeriya da ma Faransa, batun gaskiya ya fito
- Ba a samu mafita game da abin da ya biyo baya a juyin mulkin da sojin Nijar suka yi ba a watan Yulin da ya gabata
Yamai, Nijar - Hukumar sojin Nijar ta umarci jakadan Faransa ne kadai ya fice daga kasar, ba jakadun Jamus, Amurka ko Najeriya ba, in ji sanarwar da ta fitar, rahoton Anadolu Agency.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Juma'a, ma'aikatar ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa da ke nuni da cewa an kori jakadun Jamus da Amurka da Najeriya, tare da bayyana cewa, Jakadan Faransa a Nijar ne kadai aka ayyana korarsa.
Yadda batun yake na koran jakadan Faransa
A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamnatin mulkin sojan Nijar ta baiwa jakadan Faransa Sylvain Itte wa'adin sa'o'i 48 ya fice daga kasar, bisa zarginsa da kin amsa gayyatar da aka yi masa na ganawa da ministan harkokin wajen jamhuriyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar da ta hukumar fitar ta ce "Nijar ba ta bukatar izini ko tawilin yarjejeniyar Vienna ta 1961" waje ba da umarnin korar jakadan cikin sa'o'i 24.
Rikicin Nijar da matsayar Faransa
Tun bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, kasar Faransa ta nuna rashin amincewa da kuma yin Allah-wadai da abin da sojin jamhriyar ta Nijar suka aikata, rahoton Arab News.
Har yanzu ana ci gaba da cece-kuce da kai ruwa rana kan yadda za a dawo da Bazoum kan karagarsa bisa umarnin kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).
"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet
An sha bayyana yunkurin sulhu a lamarin, amma ya zuwa yanzu dai ba a warware ba kan matsayar sojin da kuma kungiyar ta ECOWAS.
Ni nake hana a farmaki sojin Nijar, - Tinubu
A bangare guda, Bola Ahmed Tinubu ya ce shi ne wanda ya jawo dakarun kungiyar ECOWAS su ka ja baya, ba su kai ga aukawa Jamhuriyyar Nijar ba.
Premium Times ta ce Shugaban Najeriyan ya nuna idan ba domin shi ba, da sojoji sun shiga Nijar da nufin dawo da mulkin farar hula a kasar.
Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da wasu malaman musulunci da ke kokari kawo zaman lafiya.
Asali: Legit.ng