Hannatu Musa Musawa: Ministar Tinubu Ka Iya Rasa Mukaminta Bayan Gano Yanzu Take Yin NYSC
- Hukumar ƴan yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta tabbatar da cewa ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, yanzu take yin bautar ƙasa
- Hukumar ta bayyana cewa Hannatu Musa Musawa ta saɓa dokarta na hana masu yin bautar ƙasa riƙe muƙamin gwamnati
- Darektan hulɗa da jama'a na hukumar ya tabbatar da cewa hukumar za ta ɗauki mataki a kan laifin da ministar ta yi
FCT, Abuja - Hukumar ƴan yi wa ƙasa hidima (NYSC), ta tabbatar da cewa ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, yanzu ta ke yin bautar ƙasarta.
Hakan ya biyo bayan zargin da ƙungiyar HURIWA ta yi na cewa ministar yanzu take yin bautar ƙasarta, yayin da take riƙe da muƙamin minista a gwamnatin Shugaba Tinubu.
Darektan hulɗa da jama'a na hukumar NYSC, Eddy Megwa, ya tabbatar da cewa ministar ƴar bautar ƙasa ce yanzu haka, cewar rahoton Daily Trust.
Darektan ya tabbatar da cewa ministar tana yin bautar ƙasarta ne a birnin tarayya Abuja, inda yanzu take cikin wata na takwas.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hannatu Musawa ta saɓa doka, NYSC
Megwa ya yi bayanin cewa riƙe muƙamin kujerar ministan da Hannatu Musawa take yi a yanzu haka ya saɓa doka, rahoton The Cable ya tabbatar.
Ya yi bayanin cewa saɓa dokar hukumar ne wani ko wata mai yin bautar ƙasa ya karɓi muƙami a gwamnati, har sai ya kammala shekara ɗaya na bautar ƙasa.
A cewar Megwa tun da farko an tura Hannatu jihar Ebonyi domin yin bautar ƙasa a shekarar 2001, amma daga baya ta dawo jihar Kaduna domin cigaba da yin bautar ƙasa.
Ya bayyana cewa lokacin da ta dawo jihar Kaduna ne ta tsere ba ta kammala bautar ƙasarta ba. Megwa ya yi nuni da cewa hukumar za ta yi duba da idon basira kan lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace.
Yan Kudancin Kaduna Na Son Minista
A wani labarin kuma, wata ƙungiya daga Kudancin Kaduna ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ba yankin kujerar minista.
Ƙungiyar ta koka kan yadda aka mayar da yankin saniyar ware inda ta buƙaci Shugaba Tinubu ya sakawa yankin da kujerar minista.
Asali: Legit.ng