Ku Gyara Matatun Cikin Gida Domin Man Fetur Ya Yi Arha, Basarake Ga FG

Ku Gyara Matatun Cikin Gida Domin Man Fetur Ya Yi Arha, Basarake Ga FG

  • Wani fitaccen Sarki a jihar Ekiti ya shawarci gwamnatin Tinubu kan yadda zata sauko da farashin man fetur a Najeriya
  • Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus Adejugbe ya buƙaci gwamnatin tarayya ta yi kokarin gyara matatun mai guda uku na ƙasar nan
  • A cewarsa ya kamata gwamnatin shugaba Tinubu ta yi amfani da kuɗin tallafin mai wajen zuba ayyukan more rayuwa

Ekiti state - Babbar Sarki wanda ake wa laƙabi da Ewi na Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, Oba Rufus Adejugbe, ya shawarci gwamnatin tararra kan tsadar man fetur.

Babban Basaraken ya yi kira ga gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ta gyara dukkan matatun man kasar nan domin kawo karshen hauhawar farashin man fetur a Najeriya.

Ewi na Ado Ekiti, Oba Adejugbe.
Ku Gyara Matatun Cikin Gida Domin Man Fetur Ya Yi Arha, Basarake Ga FG Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Sarkin ya yi wannan kiran ne a garin Ado-Ekiti a yayin wani rangadin da ya kai yankunan ci gaban kananan hukumomin Ekiti (LCDAs).

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Abun Alkairin da Zai Faru Kan Man Fetur a Karshen 2023

Wannan ziyara da ya kai yankuna na ɗaya daga cikin ayyukan bikin al'ada na “Udiroko” a wannan shekara da muke ciki 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Oba Adejugbe ya ce kudaden da ake tarawa daga cire tallafin man fetur ya kamata a yi amfani da su wajen gina ababen more rayuwa ga al'ummar Najeriya.

Yadda FG zata karya farashin litar fetur

Daga cikin irin ayyakan da ya dace gwamnatin Tinubu ta yi da kuɗaɗen a cewar basaraken har da gyaran matatun mai na cikin gida, Tribune ta rahoto.

A kalamansa, Sarkin ya ce:

“Idan aka gyara matatun mai, farashin Litar Fetur zai ragu. Ina so in yi kira ga 'yan Najeriya, na san yana da wuya; su ƙara hakuri da Gwamnatin Tarayya domin shugaban kasa yana nufin alheri ga kasa.”

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su ba da tallafi ga talakawa domin rage wahalhalun da suka tsinci kansu a ciki sakamakon cire tallafin mai.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci

A wani rahoton na daban Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Misis Mojoyinoluwa Dekalu-Thomas a matsayin shugabar hukumar NELMCO.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngalale, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 25 ga watan Agusta, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262