Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Misis Mojoyinoluwa Dekalu-Thomas a matsayin shugabar hukumar NELMCO
  • Nadin Dekalu-Thomas ya fara aiki nan take kuma za ta shafe tsawon shekaru biyar a kan kujerar
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngalale, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 25 ga watan Agusta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Misis Mojoyinoluwa Dekalu-Thomas a matsayin sabuwar Manajan Darakta kuma Shugabar hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya (NELMCO).

Shugaban kasa Tinubu ya nada shugaban NELMCO
Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Za ta shafe tsawon shekaru hudu a kan mukamin

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngalale ya sanyawa hannu kuma fadar shugaban kasa ta wallafa a manhajar X a yammacin Juma'a, 25 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ana tsaka mai wuya: Abin da Tinubu ya fadawa Malaman addini kafin su tafi Nijar

Nadin da aka yi mata zai yi aiki na tsawon shekaru hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko, Dekalu-Thomas ta yi aiki a matsayin mukaddashiyar shugabar NELMCO bayan karewar wa'adin tsohon shugaban hukumar, Adebayo Fagbemi, wanda ya kare a ranar 8 ga watan Mayun 2023.

Buhari ya nada daraktan NELMCO

Aikin wucin gadi da ta yi a baya da sabon nadin da aka yi mata yasa kujerarta na baya, babbar dataktar NELMCO ta zama babu kowa.

Shugaban kasar ya kuma amince da nadin Mista Dimla Joel Nchinney don aiki a NELMCO a matsayin babban daraktan hukumar.

An kuma bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take.

Ga wallafar a kasa:

Ministan Abuja ya karyata batun rushe gidaje 6,000 a Abuja

A wani labari na daban, ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa zai fara aikin rusa gidaje 6000 a fadin unguwanni 30 a Abuja da kuma Wadata Plaza.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Sa Labule da Rabiu Kwankwaso, Sun yi Kus-Kus a Aso Rock

Wike ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta. Ministan ya bayyana wadannan rahotanni a matsayin karya kuma cewa babu kamshin gaskiya a cikinsu.

Ya kara da cewa, bai lissafo wasu wurare ko jerin gidajen da basa bisa ka'ida da za a cire ba a FCT, maimakon haka, ya nanata bukatar cire gidajen da basa bisa ka'ida ne a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng