“Lamarin Babba Ne”: Mai Siyar Da Masara Ta Yi Shi Yanka-Yanka Don Samawa Mutane Sauki, Hoto Ya Bayyana

“Lamarin Babba Ne”: Mai Siyar Da Masara Ta Yi Shi Yanka-Yanka Don Samawa Mutane Sauki, Hoto Ya Bayyana

  • Wata mai siyar da masara da ta karkarya gasasshen masara zuwa kanana ta yi fice a soshiyal midiya
  • An gano matar tana gasa masaran siyarwa a bakin hanya, sannan aka dauki hotonta tare da yada shi a intanet
  • An rahoto cewa ta karya wasu daga cikin masaran kanana-kanana ta yadda kwastamominta da basu da karfin siyan cikakken masara za su iya siya

Wani hoto da ke yawo a Facebook ya nuno wata mai siyar da masara da ta yanka shi zuwa kanana-kana.

An gano matar zaune a bakin hanya, inda ta mayar a matsayin shagonta na siyar da gasasshen masara.

Don kowa ya iya siya, sai ta yanka masaran zuwa kanana
“Lamarin Babba Ne”: Mai Siyar Da Masara Ta Yi Shi Yanka-Yanka Don Samawa Mutane Sauki, Hoto Ya Bayyana Hoto: Facebook/Chuks Ineh da Getty Images/Abimbola Fayomi.
Asali: Facebook

Chuls Ineh wanda ya yi ikirarin cewa matar ta karkarya masaran zuwa kanana ne don kwastamominta sun daina iya siyan dindin masara, shine ya wallafa hoton a Facebook.

Kara karanta wannan

Kannywood: Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Kara Aure Ba

Mai masara ta yadu yayin da mutane suka ga yadda ta karkarya masaranta

Hakan na nufin cewa tana kokarin saukakawa kwastamominta wadanda za su zo siyan rabin masara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan har abun da Chuks ya fadi gaskiya ne kuma idan ainahin hoton daga Najeriya ya fito, lallai hakan na nufin wannan sabon abu ne da aka kirkiro tunda dai mutanen da ke siyar da gasasshen masara a Najeriya dindi suka saba siyarwa.

Masara na daya daga cikin abubuwan da ake siyarwa shekara-shekara a Najeriya, wanda ake cinsa imma gasasshe ko dafaffe.

A wasu birane kamar su Port Harcourt, ana siyar da gasasshen masara tsakanin N100 da N150 ya danganta da girmansa. Haka ma ake siyar da daffaffen masara.

Mutanen da suka ga wallafar Chuks sun yarda cewa farashin masaran da ke da arha a baya ya yi tashin gauron zabi.

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

Jama'a sun yi martani yayin da mai siyar da masara ta karkarya shi kanana-kanana

Nkem De Lightta ce:

"Ya kamata mu shiga harkar noma. Wannan ba daidai bane. Zan yi noma shekara mai zuwa. "

Oyedeji Zainab ta yi martani:

"Wannan lamari ya girmama. Shugaban kasa, kana ganin mutanenka kuwa?"

Shadrach Akumboa ya ce:

"Tawagar daidaita tattalin arziki na nan ne kawai. Wannan shine ainahin tawagar daidaita tattalin arziki."

Legit.ng ta tuntubi ainahin wanda ya wallafa hoton, Mista Chuks Ineh inda ya tabbatar da cewar lallai a Najeriya abun ya faru.

Farashin yadda ake siyar da kayayyaki a 1990 ya girgiza yan Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa yan Najeriya da dama sun yi korafin cewa abubuwa na da arha a kasar a baya, sai kuma wata budurwa yar Najeriya ta yi karin haske a kan wannan hasashe.

Adaeze Don ta wallafa wata tsohuwar takarda na siyayyar da mahaifinta ya yi a 1990 kuma farashin kayayyaki a wancan lokacin ya matukar bai wa mutane mamaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng