Wike Ya Bayar Da Umarnin Cafke Mamallakin Bene Da Ya Rufto a Birnin Taraya Abuja

Wike Ya Bayar Da Umarnin Cafke Mamallakin Bene Da Ya Rufto a Birnin Taraya Abuja

  • Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin cafke mamallakin ginin bene mai hawa biyu da ya rufto a birnin tarayya Abuja
  • Masu aikin ceto sun samu nasarar ceto mutane masu yawa da ginin ya rufto a kansu, inda aka garzaya da su zuwa asibiti
  • Wike ya nuna takaicinsa kan ruftowar ginin sannan ya bayar da umarnin a biya kuɗin maganin waɗanda suka samu raunika

FCT, Abuja - Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, ya bayar da umarnin cafke mamallakin ginin bene mai hawa biyu da ya rufto a Abuja

Ginin benen dai ya rufto ne a daren ranar Laraba, 23 ga watan Agusta, lokacin da ake ruwan saman kamar da bakin ƙwarya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Minista 1 Kan Muhimmin Batu a Villa, Bayanai Sun Fito

Wike ya umarci a cafke mamallakin benen da ya rufto a Abuja
Wike ya bayar da umarnin cafke mamallakin benen da ya rufto a Abuja Hoto: @NTANewsNow, @GovWike
Asali: Twitter

Wike ya ziyarci wurin da benen ya rufto

Ginin dai yana da aƙalla mutum 39 da ke zaune a cikinsa, inda aka tabbatar da mutuwar mutum biyu, sannan aka ceto mutum 37 inda aka garzaya da su zuwa asibitoci domin duba lafiyarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton jaridar Vanguard ya yi nuni da umarnin da Wike ya bada.

Wike yayin da yake magana a wajen ya bayyana cewa tuni aka yi wa wajen alamar za a tashe shi kuma an tsara za a ba mutanen da ke yankin diyya saboda tayar da su da za a yi daga wajen, amma hukumar FCTA ba ta biya su kuɗin ba.

A kalamansa:

"Abun takaici ne mun tashi yau da safe da labari mara daɗi na ruftowar wannan ginin benen."
"Abun takacin shi ne mun rasa rayukan mutum biyu. Ina kira ga babban sakatare ya tabbatar da cewa an samo kuɗin da za a biya kuɗin maganin mutanen da aka ceto ta yadda ba za mu ƙara rasa rayukan wasu mutanen ba, kuma cikin gaggawa za a yi hakan."

Kara karanta wannan

Minista Ya Kama Aiki Gadan-Gadan, Ya Yi Wa ‘Yan Kwangila Kaca-Kaca Daga Shiga Ofis

Wike ya yi nuni da cewa yana da matuƙar muhimmanci a gano mamallakin ginin tare da cafke shi.

Wike Ya Hana Siyar Da Masara a Abuja

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kafa sabuwar doka domin magance rashin tsaro a birnin tarayya Abuja.

Wike ya haramta siyar da kayayyaki a bakin tituna ciki har da masara, inda ya ce saide-saide na bakin hanya na taimakawa wajen matsalar tsaro a birnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng