Hukumar DSS Ta Bukaci Gwamnoni Su Mayar Da Hankali Wajen Rabon Kayan Tallafi

Hukumar DSS Ta Bukaci Gwamnoni Su Mayar Da Hankali Wajen Rabon Kayan Tallafi

  • Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta yi muhimmin kira ga gwamnonin yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Hukumar ta yi kira ga gwamnonin da su mayar da hankali wajen rabawa talakawan yankin kayan tallafi
  • A cewar hukumar rabon kayan tallafi ga talakawa zai taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron da ta daɗe tana addabar yankin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Maiduguri, jihar Borno - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ta buƙaci gwamnonin yankin da su mayar da hankali wajen rabon kayan tallafi, domin ɗorewar zaman lafiya a yankin.

Hakan na cikin matsayar da aka cimma a wajen taron darektocin hukumar na jihohi shida na yankin wanda aka yi a hedikwatar hukumar a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, cewar rahoton jaridar Leadership.

Hukumar DSS ta yi kira ga gwamnoni
Shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

Darektocin hukumar DSS na yankin sun taru ne a Maiduguri domin tattaunawa akan tsaron yankin da rawar da samun bayanan sirri za ta taka wajen yaƙi da ta'addanci, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

Darektocin DSS sun ziyarci Zulum

Darektocin a ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Abdullahi Hassan, sun ziyarci gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, bayan kammala taronsu inda suka gabatar masa da abin da suka cimmawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin Arewa maso Gabas, ya miƙa godiyarsa ga darektocin, sannan ya yi alƙawarin yin aiki tare da takwarorinsa domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Ya kuma alƙwarin tuntuɓar gwamnonin jihohin Yobe, Adamawa, Taraba, Gombe da Bauchi domin tabbatar da cewa an yi rabon kayan tallafin yadda ya dace ga talakawa.

Gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni N5bn

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana shirinta na rabawa jihohin ƙasar nan da birnin tarayya Abuja, tallafin N5bn domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Matasan Jam'iyyar a Jihar Arewa Kan Abu 1

Gwamnatin tarayyar ta cimma wannan matsayar ne bayan kammala taron majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin Kashim Shettima.

An Bukaci a Dawo Da Tallafin Man Fetur

A wani labarin kuma, gamayyar shugabannin matasan yankin Kudu maso Gabashin Najeriya (COSEY), ta zargi shugaban ƙasa Bola Tinubu kan kuɗin tallafi.

Ƙungiyar ta bayyana cewa shugaban ƙasar yana yaudarar ƴan Najeriya ne da tallafin, domin tilasta musu amincewa da ƙarn kuɗin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng