Makuden Miliyoyi: Farashin Motar Alfarma Ta Wike Mai Lamba 'FCT-01' Ya Bayyana, Yan Najeriya Sunyi Martani

Makuden Miliyoyi: Farashin Motar Alfarma Ta Wike Mai Lamba 'FCT-01' Ya Bayyana, Yan Najeriya Sunyi Martani

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi abun da ba a taba tsammani ba yayin da ya kama aiki cike da dirama
  • Hakan ya kasance ne yayin da tsohon gwamnan na jihar Ribas ya haddasa cece-kuce saboda irin motar da ya zabi hawa zuwa ofis a ranarsa ta farko
  • A ranar Talata, 22 ga watan Agusta, ministan ya isa ofis a cikin wata tsadaddiyar motar Lexus LX 600 SUV mai lamba ‘FCT – 01’

Abuja - Yanayin motar da sabon ministan Abuja da aka rantsar, Nyesom Wike ya hau zuwa wajen aiki a ranarsa ta farko a ofis ya haddasa cece-kuce.

Wike ya hau tsadaddiyar mota a ranarsa ta farko a ofis a Abuja
Makuden Miliyoyi: Farashin Motar Alfarma Ta Wike Mai Lamba 'FCT-01' Ya Bayyana, Yan Najeriya Sunyi Martani Hoo: @MobilePunch
Asali: Twitter

A ranar Talata, 22 ga watan Agusta, Wike ya isa babban birnin tarayya a cikin wata tsadaddiyar motar alfarma kirar Lexus LX 600 SUV dauke da lambar ‘FCT – 01’, kuma wannan ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakunansu.

Kara karanta wannan

"Abuja Ba Fatakwal Ba Ce": Hadimin Atiku Ya Gargadi Wike, Ya Gaya Masa Abin Da Yakamata Ya Yi

Farashin motar Wike a dalar Amurka da Naira

Jaridar Punch ta rahoto cewa wani bincike da aka yi a shafin yanar gizon kamfanin Lexus ya sako farashin wannan tsadaddiyar motar SUV din inda ya fara daga $100,115; wanda ya yi daidai da N75,764,028.55.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nawa ne $100,000.00? – dalar Amurka dubu dari daya ya kai ₦74,629,274.40 (NGN) a yau ko kuma naira miliyan saba'in da hudu da dubu dari shida da ashirin da tara da dari biyu da hudu. An yi amfani da farashin kasuwar tsakiya wajen canja dalar zuwa naira.

Saboda haka farashin motar Wike ya kai N75,764,028.55, a kudin Najeriya.

Yan Najeriya sun yi martani ga lambar motar Wike a matsayin ministan Abuja

Yan Najeriya sun garzaya manhajar X wacce aka fi sani da Twitter a baya don bayyana ra'ayinsu kan ci gaban.

Kara karanta wannan

Elon Musk Ya Samu Dala Biliyan 11 Cikin Dare Yayin Da Dangote Ya Yi Asarar Biliyan 43 A Kwana Daya

@BatifiedGeraltya rubuta:

"Kudin uba waye ya bata?"

@Mr_9izeGuy ya rubuta:

"Ya kamata ya zama FCT - 001 mana.
"Wikematics, Abuja za ku san cewa sabon Sheriff na gari."

@Deji_Dokun ya rubuta:

"Shin ya kamata Wike ya kama aiki a kabu-kabu ko tuk-tuk ne?"

Elon Musk ya samu dala biliyan 11 a dare daya

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk ya shawo kan asarar da aka kwashe makonni ana tafkawa a kasuwannin hannayen jari na duniya inda ya samu sama da dala biliyan 11 a dare daya.

Mamallakin kamfanin na X, wanda arzikinsa ya ragu bayan ya rufe da dala biliyan 200, ya sake dawowa kan kafafunsa yayin da hannayen jarin kamfanin Tesla suka farfado.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng