Fasto Kumuyi Ya Yi Sabon Hasashe Mai Kyau a Kan Shugaba Tinubu

Fasto Kumuyi Ya Yi Sabon Hasashe Mai Kyau a Kan Shugaba Tinubu

  • Fasto W.F Kumuyi ya gayawa ƴan Najeriya cewa su kwantar da hankulansu abubuwa za su daidaita a lokacin mulkin Shugaba Tinubu
  • Babban faston ya bayyana cewa ubanngiji zai yi mu'ujizoji masu yawa a wannan gwamnatin ta hanyar taɓa zuciyoyin shugabanni
  • A cewar malamin addinin, an zaɓi sabbin ministocin ne bisa lura da ayyukan da suka yi a baya sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ba su haɗin kai

Osogbo, jihar Osun - Fasto William Folorunso Kumuyi, shugaban cocin Deeper Christian Life Ministry, ya buƙaci ƴan Najeriya da su marawa gwamnatin Shugaba Tinubu baya, inda ya ƙara da cewa za a dara.

A cewar rahoton The Nation, malamin addinin ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa ubangiji zai yi mu'ujizoji a zukatan shugabanni sannan zai ba su hikimar jagorantar ƙasar nan da mayar da hankali wajen abubuwan da za su amfani al'umma.

Kara karanta wannan

"Akwai Haske": Abdulsalami Ya Yi Magana Kan Tattaunawarsu Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Fasto Kumuyi ya yi magana kan mulkin Tinubu
Fasto Kumuyi ya magantu kan mulkin Shugaba Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Babban faston ya bayyana hakan ne a birnin Osogbo, babban birnin jihar Osun, a ranar Talata, 22 ga watan Agustan 2023.

Fasto Kumuyi ya yi magana kan ministocin Tinubu

A cewar Kumuyi, sabbin ministocin na Shugaba Tinubu, an zaɓo su ne ta hanyar lura da abubuwan da suka yi a baya, daga nan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba su haɗin kai, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Mu manta da abin da ya faru a baya. Wannan sabon lokaci ne, sannan na yi amanna cewa za mu ga sabbin abubuwa ta hannun shugaban ƙasar mu da mambobin gwamnatinsa. Abubuwa masu kyau za su faru."

Fasto Kumuyi ya bayyana cewa matsayar da yake a kai ita ce ubangiji zai taɓa zuciyar shugabannin Najeriya, sannan zuciyoyinsu za su mayar da hankali wajen yin abubuwan da za su amfani ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Wike Da Sauran Ministocinsa

Ministocin Tinubu Za Su Lakume N8.63bn

A wani labarin kuma, an bayyana kuɗaden da ministocin Shugaba Tinubu za su laƙume a cikin shekara huɗu masu zuwa.

Sabbin ministocin za su laƙume N8.63bn a matsayin albashi da haƙƙoƙin da gwamnatin tarayya za ta riƙa biyansu. Ministocin na Shugaba Tinubu dai su ne dai ministoci mafi yawa da aka taɓa yi a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng