Yan Najeriya Sun Yi Martani Bayan An Bukaci Tinubu Ya Nada Dansa Minista
- Ƴan Najeriya sun yi martani kan kiran da aka yi na Shugaba Tinubu ya naɗa ɗansa Seyi Tinubu, a matsayin ministan matasa
- Wani mai amfani da sunan Jerry Koko Durojaiye a Twitter, ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya naɗa Seyi ministan matasa, inda ya ƙara da cewa ya cancanta
- A cewar Durojaiye, sama ba za ta faɗi ba idan Shugaba Tinubu ya naɗa ɗansa a matsayin minista a gwamnatinsa
An buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa ɗansa Seyi Tinubu, a matsayin ministan matasa.
Wani mai amfani da Twitter mai suna, Jerry Koko Durojaiye, shi ne ya yi wannan roƙon a shafinsa @kokomatic, a ranar Lahadi, 20 ga watan Agustan 2023.
Dalilin da yasa yakamata Tinubu ya naɗa Seyi minista
Durojaiye ya bayyana cewa Seyi Tinubu ya cancanta kuma yana da basirar da zai iya jagorantar ma'aikatar matasan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa sama ba za ta faɗo ba idan shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya naɗa Seyi a matsayin mininsta a gwamnatinsa.
A kalamansa:
"Mai girma Shugaba Bola Tinubu @officialABAT, dan Allah ka taimaka ka zaɓi ɗan ka a matsayin ministan matasa na gaba. Ya cancanta kuma yana da basira. Sama ba za ta faɗo ba ƴallabai. Nagode."
"Daga na ka, Jerry Koko."
Ƴan Najeriya sun yi martani kan kiran Tinubu ya naɗa Seyi minista
Ƴan Najeriya sun yi martani kan kiran da aka yi ga Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ɗansa, Seyi Tinubu, a matsayin ministan matasa.
@manshegzy ya rubuta:
"Wallahi sama ba za ta faɗo ba, matasa ne kawai za su shiga taitayinsu."
@itsneme ta rubuta:
"Aa ba haka za a yi ba, ina bayar da shawarar ya naɗa ɗan Seyi ne.
@YojuKunle ya rubuta:
"Saboda ya san Najeriya ba Rwanda ko Zimbabwe ba ce, ba zai ɗauki wannan shawarar ta ka ba."
@ahdsall ya rubuta:
"Tun da gwamnan jihar Osun ya sanya ƴan uwansa a gwamnatinsa, wato shi ma Tinubu sai ya yi haka ko. Ba matsala, amma kar ka manta shekara huɗu kawai zai yi a kan kujerar. Ina fatan lokacin da shugaban ƙasa na gaba ya sanya ƴan ƙauyensu kawai, ba za ku yi ƙorafi ba."
Na Hango Matsala a Mulkin Tinubu, Mbaka
A wani labarin kuma, shugaban cocin Adoration Ministry in Enugu, Nigeria (AMEN), Rabaran Fr. Ejike Mbaka, ya yi sabon hasashen kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Babban faston ya bayyana cewa ya hango wani mummunan abu na shirin fariwa a ƙasar nan idan Shugaba Tinubu bai miƙa lamuransa ga ubangiji ba.
Asali: Legit.ng