Jirgin Kaduna-Abuja: DSS Ta Kama Manajoji 2 da Wasu Jami'ai Kan Kundin Harin Yan Bindiga

Jirgin Kaduna-Abuja: DSS Ta Kama Manajoji 2 da Wasu Jami'ai Kan Kundin Harin Yan Bindiga

  • Hukumar DSS ta kama Manajan kula da zirga-zirgan jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja bayan fitar da bayanan sirri
  • Wata majiya a NRC ta bayyana cewa jami'an DSS sun cafke shi tare da Manajam ɓangaren ayyuka da wasu ma'aikata
  • A makon da ya shuɗe ne DSS ta ankarar da hukumar NRC cewa ta gano yan bindiga na ƙulla tuggun sake kai hari kan jirgin ƙasa

Abuja - Hukumar jami'an tsaron sirri (DSS) ta kama Manajan harkokin sufurin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja, Pascal Nnorli, biyo bayan fitar kundin gargaɗi kan yuwuwar farmakin 'yan bindiga.

Wata majiya mai ƙarfi a hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ƙasa ta ƙasa (NRC) ta tabbatar da kama Manajan ga wakilim jaridar Punch bisa sharaɗin ɓoye bayananta.

Jami'an hukumar farin kaya DSS.
Jirgin Kaduna-Abuja: DSS Ta Kama Manajoji 2 da Wasu Jami'ai Kan Kundin Harin Yan Bindiga Hoto: punch

Majiyar ta bayyana cewa jami'an DSS sun cafke Manajan tare da Manajan sashin ayyuka Victor Adamu, da wasu jami'an tashar jirgin Kaduna-Abuja, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Badakalar N6.9bn: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Da Ta Hannun Daman Emefiele Ta Shigar Da DSS

A ranar Laraba ta makon da ya gabata, DSS ta ankarar da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen kasa kan yunƙurin yan bindigan jeji na sake kai hari kan jirgin Kaduna-Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani kundi mai ɗauke da sa hannun daraktan DSS mai kula da shiyyar Abuja, R.N. Adepemu, hukumar ta gargaɗi Fasinjojin jirgin ƙasan da su yi takatsantsan da tsaron lafiyarsu.

Waɗanne mutane DSS ta kama?

Da take jawabi ga wakilin jaridar ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta, 2023, majiyar NRC ta ce:

"Shin kuna da masaniyar sun damƙe Manajan mu tun ranar Alhamis da ta gabata? Manajojin mu biyu, mai kula da ɓangaren ayyuka da kuma Mista Pascal, amma zuwa yanzu sun sako mutum ɗaya."
"Lamarin ya rutsa da Mista Victor ne saboda sun tarad da shi a ofishin Pascal, shiyasa suka kama shi tare da dukkan ma'aikatan Manaja Pascal kana suka tisa ƙeyarsu zuwa ofishin DSS. Har yanzun Pascal na hannunsu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnatin Kano Da Ba Alkalai Cin Hancin N10m, Ta Bayar Da Dalilai

Meyasa DSS ta kama manyan jami'an NRC?

Majiyar ta ƙara da cewa wannan kamen ba zai rasa nasaba da fitar kundin DSS na bayanan sirrin yuwuwar sake kai hari kan jirgin ƙasan Kaduna-Abuja ba, wanda ya fita ta bayan fage.

Kundin, wanda ke ƙunshe da cikakkun bayanai masu muhimmanci kan lamarin, an aika shi zuwa babban Manajan NRC.

Bugu da ƙari, DSS ta yi gargaɗin cewa idan wannan bayanin ya fita duniya ta sani, to hakan ka iya tilasta wa hukumar kama duk mai hannu a sakin bayanan.

Sai dai yayin da aka tuntuɓi babban Manajan NRC, Fidet Okhiria, kan wannan batu, bai yarda ya furta komai ba.

DSS Ta Titsiye SSG Na Ogun

A wani rahoton kuma Hukumar DSS ta fara bincikar sakataren gwamnatin jihar Ogun, Tokunbo Talabi, na hannun daman gwamna Dapo Abiodun.

Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da ke kansa na hannu a buga takardun zaɓe da kuma badaƙalar tallafin annobar korona.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Wata Jiha Sun Yi Awon Gaba Da Wasu Ma'aurata

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262