An Bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Ya Yi Murabus

An Bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Ya Yi Murabus

  • Ƙungiyar Niger Delta Women League (NDWL) ta soki abubuwan da shugabaɓ majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi a baya
  • Ƙungiyar NDWL ta buƙaci Akpabio da ya yi murabus bayan katoɓarar da ya yi a wajen zaman majalisa
  • Sun bayyana zaman Akpabio shugaban majalisar dattawa a matsayin babban abun kunya ga Najeriya da yankin Neja Delta

An buƙaci shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da ya gaggauta yin murabus daga muƙaminsa.

Ƙungiyar Niger Delta Women League (NDWL), ita ce ta yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta ci karo da ita a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta.

An bukaci Akpabio ya yi murabus
An Bukaci Akpabio ya sauka daga shugabancin majalisar dattawa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Dalilin da yasa Akpabio yakamata ya yi murabus

A cikin sanarwar wacce shugabar ƙungiyar, Hon. Sheila Abiye Tamuno da manyan ƙusoshi 10 suka rattaɓawa hannu, sun caccaki Akpabio kan katoɓarar da yake a lokacin zaman majalisa.

Kara karanta wannan

An Bayyana Lokacin Da Shugaba Tinubu Zai Rantsar Da Ministocinsa Domin Fara Aiki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun bayyana zaman Akpabio shugaban majalisar dattawa a matsayin abun kunya ga Najeriya da yankin Neja Delta, saboda tarihin cin hanci da yake da shi a baya.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A ce mutumin da mutumin da a ke bincike kan cin hanci da rashawa an ɗauki kujerar shugaban majalisar dattawa an ba shi, lallai wannan wasan kwaikwayon ya yi yawa. Hakan ya mayar da ƙasarmu abun dariya a wajen ƙasashen duniya."

Ƙungiyar ta buƙaci majalisar dattawa da ta yi abin da ya dace ta hanyar tabbatar da an tsige Akpabio, idan ya ƙi yin murabus.

Ƙungiyar za ta yi zanga-zanga

Sun kuma yi barazanar tattaro mata miliyan ɗaya zuwa majalisar dattawa domin yin zanga-zanga, idan har tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya ƙi yin murabus daga muƙaminsa.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari a Jihar Neja

A kalamansu:

"Za mu tattaro matan yankin Neja Delta miliyan ɗaya a ranar 26 ga watan Satumban 2023, zuwa ƙofar majalisar dattawa domin yin godiya ga ƴan majalisar ko matsa musu lamba su yi abin da ya dace."

Akpabio Ya Yabi Peter Obi

A wani labarin na daban kuma, shugaban majalisar dattawa ya yabi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.

Sanata Godswill Akpabio ya yabi ɗan takarar ne bisa halartar ɗaurin auren ɗan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda aka yi a birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng