Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 5 a Wani Farmaki a Wasu Kauyukan Jihar Katsina

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 5 a Wani Farmaki a Wasu Kauyukan Jihar Katsina

  • Miyagun ƴan bindiga sun addabi ƙauyukan ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina da hare-hare
  • Ƴan bindigan sun halaka mutum biyar a yayin harin tare da sace dabbobi da mata masu yawa zuwa cikin daji
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin inda ta bayyana cewa jami'anta na ƙoƙarin cafko miyagun

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai hare-hare a ƙauyukan ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.

Ƴan bindigan a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 1:00 na rana sun halaka wani bawan Allah mai suna Rabilu Tukur, a ƙauyen Dan Ali cikin ƙaramar hukumar Danmusa, cewar rahoton Daily Trust.

Yan bindiga sun halaka mutane masu yawa a jihar Katsina
Yan bindigan sun farmaki kauyuka masu yawa a Katsina Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Yadda harin ya auku

Wani mazaunin ƙauyen Dan Ali, ya bayyana cewa mamacin wanda ma'aikaci ne a ƙaramar hukumar Danmusa, yana kan hanyarsa ta dawowa gida ne bayan ya kai wani fasinja ƙauyen Tashar Biri.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bi Tsakar Dare Sun Sace Matar Wani Babban Malamin Addini a Jihar Kwara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yana amfani da babur ɗinsa wajen yin Achaɓa. Ya kai wani fasinja zuwa Tashar Biri, yana kan hanyar dawowarsa ƴan bindigan suka biyo shi suka halaka shi bayan sun farmake shi da adda da tsakar rana." A cewarsa

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun biyo mutanen ƙauyen da suka dawo Dan Ali da dabbobinsu domin tsira, inda suka sace musu dabbobi masu yawa.

Ƴan bindigan sun farmaki wasu ƙauyukan

Haka kuma a ranar Juma'a, ƴan bindiga sun farmaki ƙauyen Maidabino a ƙaramar hukumar Danmusa, inda suka riƙa shiga gida-gida, suka halaka mutum ɗaya, suka sace matarsa tare da dabbobinsa.

Wani mazaunin Maidabino ya bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, suka farmaki gidaje da dama tare da halaka wani mutum ɗaya da ya ɓoye a cikin banɗakinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Atiku, Obi: An Gargadi Kotun Zaben Shugaban Kasa Kan Yin Hukuncin Da Zai Haifar Da Rikici a Kasa

"Abun takaicin shi ne akwai sojoji da a ka ajiye a makarantar sakandiren gwamnati da ke ƙauyen waɗanda aka sanar da su dangane da harin, amma ba su zo ba har sai da ƴan bindigan suka bar ƙauyen." A cewarsa.

Ya ƙara da cewa a ranar Juma'an, ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Sabon Garin Unguwar Ganau, inda suka halaka mutane uku tare da yin awon gaba da mata masu yawa.

Yan sanda sun yi bayani

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da aukuwar harin na ƙauyen Dan Ali inda aka halaka mutum ɗaya.

Ya bayyana cewa cewa jami'an rundunar sun bazama domin cafko miyagun ƴan bindigan da suka aikata ta'addancin.

Yan Sanda Sun Sheke Dan Ta'adda a Katsina

A wani labarin kuma, ƴan sanda sun samu nasarar ɗaƙile harin ƴan ta'adda a ƙauyen Korogo cikin ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Jajirtattun ƴan sandan sun sheƙe ɗan ta'adda ɗaya a yayin artabun tare da ƙwato muƙamai masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng