Gwamnatin Jihar Akwa Ibom Ta Bayyana Gaskiya Kan Batun Kin Dawo Da Jirgin Gwamnati Da Tsohon Gwamna Ya Yi
- Wani hadimin gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, ya bayyana dalilin da yasa gwamnan ya hau jirgin ƴan kasuwa a maimakon na gwamnati
- Ya bayyana cewa gwamnan yana ƙoƙarin cika alƙawarinsa ne na bunƙasa kasuwancin da jihar ke da hannun jari a ciki ne
- Hadimin ya yi fatali da batun cewa jirgin gwamnatin jihar har yanzu yana a hannun magabacinsa
Akwa Ibom, Uyo - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta yi martani kan raɗe-raɗin cewa tsohon gwamna Emmanuel Udom ya ƙi dawo da jirgin saman gwamnatin jihar.
Raɗe-raɗin sun yi ta yawo ne bayan cikin ƴan kwankin nan an nuna gwamnan jihar, Umo Uno, ya hau jirgin ƴan kasuwa (Ibom Air) daga Uyo babban birnin jihar zuwa birnin tarayya Abuja.
An tattaro cewa gwamna Uno sai da aka bincike shi tas kamar yadda ake yi yi wa sauran mutanen da za su hau kan jirgin ƴan kasuwa.
Da yake bayyana gaskiyar yadda lamarin yake, babban mai ba gwamnan shawara kan bincike-bincike, Mr Essien Ndueso, ya bayyana cewa jirgin da gwamnan yake amfani da shi, ba ya hannun magabacinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mr Ndueso ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da wani gidan rediyo, a ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta.
Dalilin gwamna Uno na hawa jirgin Ibom Air
Ya bayyana cewa gwamnan ya yanke shawarar hawa jirgin ne saboda cika alƙawarinsa na tallafa wa kasuwancin da gwamnatin jihar ke da hannun jari a ciki da na ƴan jihar domin taimaka musu sj ƙara bunƙasa.
Ya ƙara da cewa raɗe-raɗin da a ke yaɗa wa cewa har yanzu jirgin gwamnatin jihar na hannun tsohon gwamna Emmanuel Udom, abun takaici ne.
Mr Ndueso ya bayyana cewa raɗe-raɗin soki burutsu ne kawai da a ka shirga domin ɓata wa ubangidansa suna
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ya yi takaicin yadda jama'a ba su fahimci kyakkgawar niyyar da gwamnan ya yi ba.
Ya buƙaci jama'a da su yi fatali da raɗe-raɗin ƙarya da a ke yaɗa wa dangane da labarin.
Gwamna Uno Ya Sake Nada Tsaffin Kwamishinoni
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya sake naɗa kwamishinonin tsohon gwamnan jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa ya sake naɗa kwamishinonin ne saboda da su ga yi faɗi tashi wajen yaƙin neman zaɓe.
Asali: Legit.ng