Godswill Akpabio Ya Yaba Da Zuwan Peter Obi Wajen Daurin Auren Dan Sanata Barau Jibrin

Godswill Akpabio Ya Yaba Da Zuwan Peter Obi Wajen Daurin Auren Dan Sanata Barau Jibrin

  • Shugaban majalisar dattawa ya yaba sosai bisa halartar ɗaurin auren ɗan Sanata Barau da Peter Obi ya yi
  • Sanata Godswill Akpabio ya bayyana zuwan Peter Obi wajen ɗaurin auren a matsayin alamun da ke nuna akwai haɗin kai a ƙasar nan
  • Ɗaurin auren na Abdullahi Barau da amaryarsa Bilkisu Aliyu Sani Madaki, ya samu halartar manyan ƙusoshi a ƙasar nan

Jihar Kano - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ji daɗin zuwan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi wajen ɗaurin auren ɗan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau.

A jiya Juma'a, 18 ga watan Agusta aka ɗaura auren ɗan Sanata Barau, Abdullahi Barau da amaryarsa Bilkisu Aliyu Sani Madaki, a masallacin Juma'a na Isyaku Rabiu da ke birnin Kano.

Kara karanta wannan

Jerin Ma'aikatu 10 Masu Muhimmanci a Gwamnatin Tinubu, Da Sunayen Ministocin Da Za Su Jagorancesu Da Jihohinsu

Akpabio ya magantu kan zuwan Peter Obi Kano
Godswill Akpabio ya yabi Peter Obi kan zuwa wajen daurin auren dan Sanata Barau Hoto: @SPNigeria
Asali: Twitter

Ɗaurin auren ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Akpabio ya magantu kan zuwan Peter Obi

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana zuwan Peter Obi wajen ɗaurin auren a matsayin wani alamu na samun haɗin kai a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio wanda ya yi magana bayan kammala ɗaurin auren a Kano ranar Juma'a, ya ƙara da cewa halartar manyan ƙusoshi zuwa wajen ɗaurin auren ya nuna cewa, Sanata Barau mutum ne na mutane.

"Ka ga a nan har ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi da tawagarsa suna wannan wajen, hakan ya nuna cewa Najeriya za ta cigaba da zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya." A cewarsa.

Ɗan Sanata Barau ya angonce

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya zama waliyyin ango, shi ne ya jagoranci ƙusoshin jam'iyyar APC a wajen ɗaurin auren.

Kara karanta wannan

Wike Da Wasu Ministocin Tinubu 3 Da Suka Rike Muƙami a Gwamnatin Buhari Da Ta Jonathan

Kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas, shi ne ya zama waliyyin amarya, Bilkisu Aliyu Sani Madaki, ɗiyar mataimakin marasa rinjaye na majalisar wakilai, Aliyu Sani Madaki.

Babban limamin masallacin Juma'a na Isyaku Rabiu, Sheikh Abdullahi Mahmud Salga, shi ne ya ɗaura auren kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

SERAP Ta Maka Akpabio Kotu

A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta shigar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ƙara a gaban kotu.

Ƙungiyar ta maka shugaban majalisar dattawan ne bayan ya yi suɓutar bakin cewa majalisar ta tura wa Sanatoci kuɗaɗen shaƙatawa a lokacin hutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng