ECOWAS Ta Ce Sojojinta Sun Shirya Tsaf Don Afkawa Jamhuriyar Nijar

ECOWAS Ta Ce Sojojinta Sun Shirya Tsaf Don Afkawa Jamhuriyar Nijar

  • Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS ta saka ranar da za su afkawa Jamhuriyar Nijar da yaki
  • Kungiyar ta ce a yanzu sojojin ECOWAS sun shirya tsaf jiran umarni kawai su ke daga sama don daukar mataki
  • ECOWAS a baya ta ba wa sojojin Nijar wa'adin mako da su mika mulki ga Bazoum amma abin ya ci tura

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta saka ranar da za ta kai farmaki Jamhuriyar Nijar.

ECOWAS ta himmatu wurin mayar da hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

ECOWAS ta shirya sojojinta tare da saka ranar afkawa Nijar
ECOWAS Ta Bayyana Cewa Sojojinta Sun Shirya Afkawa Nijar. Hoto: France 24.
Asali: Facebook

Wane hukunci ECOWAS ta dauka?

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar ECOWAS ta yi zama a birnin Accra ta kasar Ghana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

ECOWAS Ta Shawarci Sojojin Juyin Mulkin Nijar Bayan Wani Hari Da 'Yan Bindiga Suka Kai Mu Su

Kungiyar ta yanke hukuncin daukar matakin soji a kan Nijar inda su ka ce sojojin su na shirye don jiran umarni, RFI ta tattaro.

ECOWAS ta fi mai da hankali kan mayar da Bazoum kujerarsa inda suka dauki aniyar daukar matakin soji muddin sojojin su ka ki yarda a yi zaman sulhu.

Kwamishinan Tsaro da Zaman Lafiya na ECOWAS Abdel-Fatau Musah ya ce idan dukkan hanyoyin su ka gaza, dakaru a shirye su ke zuwa filin daga.

Wane dama ECOWAS ta ba wa sojin Nijar?

Har ila yau, ya ce sun ba da damar diflomasiyya ga sojojin Nijar don daidaito kafin a kai ga afkawa da karfin soji, cewar Channels TV.

A cewar rahotanni, ECOWAS ta mika duk wata ta yi ga sojojin Nijar ba tare da son daukar matakin soji ba.

Kungiyar na neman a dawo da Bazoum kan kujerarsa cikin lumana wanda har yanzu sojojin Nijar din sun yi biris da bukatar.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Tura Zazzafan Sako Ga ECOWAS, Tinubu Kan Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

A baya kungiyar ta ba wa sojojin mako daya da su mika mulki ga Bazoum ko su fuskanci barazana.

ECOWAS Ta Ba Wa Sojin Nijar Wa'adin Mako 1 Da Su Mika Mulki

A wani labarin, kungiyar ECOWAS ta ba wa sojojin Nijar wa'adin mako da su yi gaggawar mika mulki ga hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum.

Kungiyar ta ce idan ba su bi wannan umarni ba za su fuskanci takunkumi da ya hada da daukar matakin soji.

A bangarensu, sojojin sun yi fatali da umarnin tare da shan alwashin ci gaba da rike madafun iko a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.