Jami’an Sojoji 36 Aka Kashe a Jihar Neja, Inji Hedkwatar Tsaro

Jami’an Sojoji 36 Aka Kashe a Jihar Neja, Inji Hedkwatar Tsaro

  • Hedkwatar tsaro ta yi martani a kan kisan gillar da yan ta'adda suka yi wa dakarun sojoji a wani harin kautan bauna
  • Kakakin hedkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa dakarun sojoji 36 yan ta'adda suka kashe a jihar Neja
  • Sai dai kuma, Buba ya ce ana kan gudanar da bincike don gano abun da ya haifar da hatsarin jirgin soji a wannan rana

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, Hedkwatar tsaro, ta bayyana cewa jami'an sojoji 36 aka kashe a jihar Neja.

Darektan watsa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayyana adadin mutanen da aka kashe a harin kautan baunar da aka kaiwa sojoji a jihar ta arewa maso gabas a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe

Sojoji 36 aka kashe a jihar Neja
Hoto: Patrick Meinhardt/AFP. An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton.
Asali: Getty Images

Ku tuna cewa wani jirgin sojoji ma ya yi hatsari a wannan ranar.

Daily Trust ta rahoto cewa an bayar da cikakken bayani kan mummunan al'amarin ne a yayin taron manema labarai da aka saba yi sau biyu a mako.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hedkwatar tsaro na bincike don gano musababbin hatsarin jirgin soji

Da aka tambaye shi game da ainahin abun da ya haddasa hatsarin jirgin, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musababbin abun sannan ya bukaci jama'a da su yi hattara da farfagandar ‘yan ta’adda, sannan su ci gaba da zama masu kishin kasa.

Ba a taba sojoji a ci bulus, DHQ

Ya kuma sha alwashin cewa babu kungiyar da za ta iya farmakar dakarun sojojinta sannan ta ci bulus.

Buba ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Emefiele Ya Isa Kotu Domin Fuskantar Tuhume-Tuhumen Da Ake Yi Ma Sa

“Babu kungiyar da za ta farmaki dakarunmu ba tare da ta wani mummunan sakamako ba.”

Yan ta'adda sun yi wa dakarun sojoji kautan bauna a yankin Zungeru da ke jihar, kuma wasu dakarun sojin Najeriya da dama sun kwanta dama a harin.

Hakazalika, jirgin sojojin sama mai lamba MI-171 da ya je aikin kwashe wanda aka kashen ya yi hatsari a ranar Litinin a karamar hukumar Shiroro da ke jihar.

Legit.ng ta tuntubi wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa don jin yadda ake ciki tun bayan harin da aka kai wa sojojin inda ya ce suna cikin fargaba har yanzu.

Ya ce:

“Gaskiya abun babu dadi kuma mun shiga tashi hankali, jama’a sun koma bakin harkokinsu amma dai har yanzu cikin dar-dar muke don rashin sanin abun da zai iya kaiwa ya komo. Muna dai rokon Allah ya kawo mana dauki a wannan hali da kasarmu ke ciki na fama da rashin tsaro.”

Kara karanta wannan

DSS: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Shirin Kai wa Mutane Mugun Hari a Jirgin Abuja-Kaduna

Sojojin sun yi yunƙurin tare 'yan ta'addan da suka sato shanu

Da farko mun ji cewa sojoji 13 ne aka kashe a ranar Lahadi, yayinda kuma aka kashe 8, cikinsu har da Kyaftin ɗaya da kuma Manjo ɗaya a harin kwanton ɓaunar da ya wakana ranar Litinin.

Rahoton ya bayyana cewa sojojin sun yi yunkurin tare 'yan ta'addan ne da aka ce sun sato shanu masu tarin yawa a wani ƙauye mai suna Kundu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel