Yan Sanda Sun Dakile Harin 'Yan Ta'adda a Jihar Katsina
- Ƴan sanda sun samu nasarar daƙile harin ta'addancin da ƴan ta'adda suka kai a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina
- A lokacin fafatawar da jami'an ƴan sandan suka yi da ƴan ta'addan, an tura ɗan ta'adda guda ɗaya zuwa barzahu
- Jami'an ƴan sandan sun kuma ƙwato makamai da tumakai masu yawa da ƴan ta'addan suka sace a ƙauyen
Jihar Katsina - Jami'an ƴan sanda a jihar Katsina sun daƙile harin ƴan ta'adda a ƙauyen Korogo, cikin ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Jami'an ƴan sandan sun halaka ɗan ta'adda ɗaya a yayin artabun da suka yi da ƴan ta'addan, cewar rahoton Vanguard.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce ƴan sandan sun ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan.
Ƴan sandan sun ƙwato makamai
A cewarsa jami'an ƴan sandan sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47, harsasai 110 da tumakai 60 da ƴan bindigan suka sace a ƙauyen, rahoton The Punch ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar na cewa:
"A ranar 15 ga watan Agustan 2023, da misalin ƙarfe 9:00 jami'an ƴan sanda sun samu kiran gaggawa cewa ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun farmaki ƙauyen Korogo cikin ƙaramar hukumar Jibia inda suka sace tumakai 60."
"Bayan samun rahoton, cikin gaggawa DPO na Jibia ya tura tawagar jami'an ƴan sanda zuwa ƙauyen inda suka yi musanyar wuta da ƴan bindigan, wanda a dalilin haka aka tilasta musu guduwa zuwa cikin daji."
"A yayin da ake duba inda aka yi artabun, an yi arba da gawar wani ɗan ta'adda ɗaya, sannan an ƙwato tumakai 60 da aka sace da bindiga ɗaya ƙirar AK 47 da harsasai 110. Ana ci gaba da gudanar da bincike."
'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki Jihar Arewa, Sun Salwantar Da Rayuka Da Sace Bayin Allah Masu Yawa
Yan Bindiga Sun Sace Mutane Masu Yawa a Zamfara
A wani labarin na daban kuma, miyagun ƴan bindiga sun sace mutane masu yawa a wani sabon harin da suka kai a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan waɗanda suka ɓadda kama cikin shiga irin ta mata sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi bayan sun dira a garin na Maru.
Asali: Legit.ng