Darekta Janar Na Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar Ya Rasu
- Muhammad Dakat, wani sanannen na hannun daman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya rasu
- Dakat masoyin Atiku ne kuma a baya ya taɓa riƙe Darekta Janar na ƙungiyar National Solidarity Movement for Atiku/Ifeanyi Okowa (NSM)
- Atiku cike da jimami ya aike da saƙon ta'aziyyarsa a soshiyal midiya kan wannan babban rashin da ya yi na ɗaya daga cikin magoya bayansa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Muhammad Dakat, Darekta Janar (DG) na ƙungiyar National Solidarity Movement for Atiku/Ifeanyi Okowa (NSM), ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi Muhammad ɗan a mutun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ne.

Source: Twitter
Atiku ya aike da saƙon ta'aziyya
Labarin mutuwar Muhammad ya riski ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a ranar Talata, 15 ga watan Agustan 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cikin wata sanarwa da Atiku ya rattaɓawa hannu, ya bayyana cewa:
"Yanzu na ke samun labarin rasuwar Muhammad Dakat."
"A matsayin Darekta Janar na ƙungiyar National Solidarity Movement for Atiku/Okowa (NSM), Muhammad ya sanya ƙwazo da jajircewa kan aikin nemo ƴan ƙasa a lokacin zaɓen da ya gabata."
"Ko a bayan an kammala zaɓe, bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen aikinsa. Muhammad abun koyi ne ga matasa sannann shugaba wanda yake jagorancinsa bisa amanna da abinda ya yarda da shi."
"Mun yi rashin ɗaya daga cikin manyan mambobin tafiyar Atikulated yana matashinsa."
"Ifeanyi Okowa da ni, a madadin tawagar mu, muna miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyalai da abokan Dakat, ƙungiyar NSM da mambobin ƙungiyoyin da ke goyon bayan mu gaba ɗaya."
"Za a yi matuƙar kewarsa. Ina addu'ar Allah ubangiji ya ba iyalansa juriyar wannan rashin da suka yi. Allah ya albarkaci abin da ya bari. Ameen."

Kara karanta wannan
"Abun Kunya": 'Yan Najeriya Sun Fusata Bayan Ganin Dakarun Tsaro Na Musamman Da Ke Gadin Seyi Tinubu
Sanatan Najeriya Ya Rasu
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa wani babban sanatan Najeriya ya kwanta dama a ƙasar Amurka, bayan ya yi fama da matsananciyar jinyar rashin lafiya.
Sanata Annie Okonkwo ya yi bankwana da duniya yana da shekara 63. Marigayin ya yi sanatan Anambra ta Tsakiya a majalisar dattawa daga shekarar 2007 zuwa 2011.
Asali: Legit.ng
