'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojoji 20 a Harin Kwanton Bauna a Jihar Neja

'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojoji 20 a Harin Kwanton Bauna a Jihar Neja

  • Sojoji aƙalla 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wata arangama da 'yan bindiga a Neja
  • Hakan ya faru ne a wani hari na kwanton ɓauna da 'yan bindigar suka kai wa sojojin da ke bakin aiki
  • Sojojin sun yi yunƙurin tare 'yan ta'addan da suka sato shanu masu tarin yawa a wasu ƙauyuka da ke jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Neja - Aƙalla sojojin Najeriya 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani mummunan harin kwanton ɓauna da 'yan ta'addan jeji suka kai mu su a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina da ke jihar Neja.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadin da ta gabata kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Sojoji 20 sun rasa rayukansu a jihar Neja
Sojoji aƙalla 20 ne 'yan ta'adda suka halaka a harin kwanton ɓauna a Neja. Hoto: Naija News
Asali: UGC

Yadda 'yan ta'adda suka kashe sojoji 20 a Neja

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari a Jihar Neja

Majiya mai ƙarfi ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa wasu ƙauyuka da 'yan ta'addan suka farmaka a ƙaramar hukumar Wushishi da ke jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An bayyana cewa a ranar Juma'a da ta gabata ne 'yan ta'adda suka farmaki ƙauyukan, wanda hakan ya tilastawa mazaunansu yin hijira zuwa garuruwan Zungeru da kuma Wushishi.

Rundunar soji ta bayyana cewa mutane 18 da aka kashe, jami'an rundunar sojin ƙasa ne, yayin da biyu daga cikinsu kuma sojojin sama ne.

Sojojin sun yi yunƙurin tare 'yan ta'addan da suka sato shanu

Rahoton Channels TV ya nuna cewa sojoji 13 ne aka kashe a ranar Lahadi, yayinda kuma aka kashe 8, cikinsu har da Kyaftin ɗaya da kuma Manjo ɗaya a harin kwanton ɓaunar da ya wakana ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Masanin Tsaro Ya Bayyana Mutanen Da Ke Da Hannu a Ta'addancin Da Ke Faruwa a Najeriya

Rahoton ya bayyana cewa sojojin sun yi yunkurin tare 'yan ta'addan ne da aka ce sun sato shanu masu tarin yawa a wani ƙauye mai suna Kundu.

Wani daga cikin 'yan sa kai mai suna Sani Adamu da ya samu raunuka, ya bayyana cewa makaman da ke hannun 'yan ta'addan sun fi nasu ƙarfi.

Sanatan da ke wakiltar Neja ta Gabas a Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Mohammed Sani Musa, ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta ɗau matakin kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a yankin.

'Yan bindiga sun kashe mutane 17 a jihar Filato

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani mummunan harin 'yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar mutane 17 a jihar Filato.

Mummunan lamarin dai ya faru ne a garin Heipang cikin daren ranar Laraba, wayewar garin ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng