Kamfanin NNPC Ya Magantu Kan Rade-Radin Kara Kudin Man Fetur

Kamfanin NNPC Ya Magantu Kan Rade-Radin Kara Kudin Man Fetur

  • Kamfanin NNPC ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da rahotanni kan shirin kara farashin man fetur
  • NNPC ya bayyana haka ne yayin da yake martani ga rahotanin cewa ana sabbin shirye-shirye don kara farashin fetur daga N617 zuwa N720 ko 750 kan kowace lita
  • Da yake martani a ranar Litinin a Abuja, kamfanin na NNPC ya bukaci kwastamominsa da su yi watsi da rade-radin da ake yi a wasu wurare

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya jaddada cewar baya da niyar Kara farashin man fetur.

Kamfanin NNPC ya ce ba zai kara farashin mai ba
Kamfanin NNPC Ya Magantu Kan Rade-Radin Kara Kudin Man Fetur Hotp: NNPC Limited
Asali: Facebook

"Babu niyyar kara farashin man fetur", NNPC a kara tabbatarwa

Kamfanin na NNPC a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter ya yi watsi da rahotannin kafofin watsa labarai cewa farashin man fetur zai karu zuwa tsakanin N680 da N750 kan kowace lita daya a makonni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

A wani yunkuri na karyata jita-jitan a kan lokaci, NNPC ya jaddada cewar babu wani niya da ake yi na kara farashin zuwa sama haka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya ku kwastamominmu, mu a NNPC muna mutunta cinikinku, kuma ba mu da niyan kara farashin man fetur dinmu kamar yadda ake ta yayatawa. Don Allah ku siya ingantattun kayayyaki a farashi mai rahusa a gidajen manmu na NNPC a fadin kasar," NNPC ya rubuta."

Jama'a sun yi martani

@jennyresse ya rubuta:

"Ya aka yi kuka zama kamfani mai zaman kansa ba tare da izinin mutanen Najeriya ba?
"Wa ya ba mu amincewar siyar da kadarorin kasarmu don ku samu masu hannun jari?"

@realTobiAkinbo ya ce:

"Hakan na nufin, za ku Kara farashin man fetur, duk san da kuka karyata, a karshe sai ku aikata hakan, labarin ya bayyana a lokacin da ba ku da niyan karawa tukuna, shiyasa kuke karyata shi."

Kara karanta wannan

Ma'aikacin JAMB Ya Shiga Tasku Bayan Kama Shi Da Satar Kwamfuta Don Biyan Kudin Haya, Ya Gamu Da Hukuncin Kotu

@Engr_Stanley_EC ya ce:

"Duk abun da NNPC ya karyata shine yake zama gaskiya! Na dauki hoton wallafar Nan don yin raddi a gaba." @Kay_kay4u ya ce:
" Wanda kuka kara shin kun sanar da mu?"

NLC: Idan Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki

A wani labarin, kungiyar NLC ta ‘yan kwadagon Najeriya ta na barazanar rufe ko ina da yajin aiki muddin aka ji farashin man fetur ya sake wani sabon tashi.

Rahotanni daga This Day sun tabbatar da cewa shugaban kungiyar NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero ya nuna ba za su lamunci karin farashi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng