Gwamna Abba Kabir Na Kano Ya Bukaci 'Yan Sanda Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Masu Kwacen Waya a Jihar

Gwamna Abba Kabir Na Kano Ya Bukaci 'Yan Sanda Su Kara Kaimi Wajen Yaki Da Masu Kwacen Waya a Jihar

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya nemi jami'an 'yan sandan jihar su sake dagewa wajen yaƙi da masu laifi
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Sufeto Janar na 'yan sanda Kayode Egbetokun a ofishinsa
  • Ya jinjinawa 'yan sandan bisa yadda suke aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami'ai wajen tabbatar da tsaro a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci jami'an hukumar 'yan sanda su sake ɗaura ɗamarar yaƙi da dabanci, fashi da makami, ƙwacen waya da sauran ayyukan laifi a jihar Kano.

Ya yi kiran ne a lokacin da ya karɓi baƙucin Sufeto Janar na 'yan sanda na wucin gadi, Kayode Egbetokun da tawagarsa a ofishinsa kamar yadda sakataren yaɗa labaransa Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Ya Bayyana Hanya 1 Da Za a Iya Tsige Shugaba Tinubu

Abba Gida Gida ya jinjinawa 'yan sandan jihar Kano
Abba Kabir Yusuf ya buƙaci 'yan sanda su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da dabanci da masu ƙwacen waya. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa
Source: Facebook

Abba ya jinjinawa 'yan sandan jihar Kano

Yayin da yake yabawa jami'an 'yan sandan bisa ƙoƙarin da suke wajen yaƙi da masu laifi, ya buƙaci jami'an da su ƙara ƙaimi wajen tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abba ya kuma jinjinawa rundunar 'yan sandan bisa ƙoƙarin haɗa gwiwa da suke yi da sauran jami'ai domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya kuma shaidawa Sufeton cewa yanzu haka gwamnatinsa na gina manyan ofisoshin 'yan sanda huɗu a sassa daban-daban na birnin Kano.

Za a ƙaddamar da jami'an 'yan sanda na musamman a Kano

Sufeton 'yan sandan, wanda ya biyo ta Kano ne a kan hanyarsa ta zuwa yaye sabbin jami'ai a makarantar 'yan sanda da ke Wudil, ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Kano ga hukumar 'yan sanda.

Ya jinjinawa Gwamna Abba Kabir bisa ƙoƙarin samar da duk kayayyakin da jami'an 'yan sandan jihar Kano ke buƙata wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Hankalin Babban Gwamnan Jam'iyyar PDP Ya Tashi Bisa Zargin Yunkurin Yi Ma Sa Juyin Mulki

Sufeton ya kuma shaidawa gwamnan Kano cewa yanzu haka hukumar 'yan sandan na yunƙurin ƙaddamar da wasu jami'ai na musamman, wanda a jihar Kano ne za a fara kaddamar da irinsu.

Ƙasurgumin Dan daba ya miƙa kansa ga 'yan sanda a Kano

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani ƙasurgumin ɗan daba da ake nema ruwa a jallo, da ya yi wa kansa ƙiyamullaili, ta hanyar miƙa kansa wurin hukumar 'yan sandan jihar Kano.

Nasiru Abdullahi, wanda aka fi sani da Chile Mai Doki, ya miƙa kansa biyo bayan ayyana sunansa cikin mutane uku da rundunar ta sanya kyautar kuɗi ga duk wanda ya kawo su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng