Yan Bindiga Sun Kona Fadar Wani Babban Basarake a Jihar Imo
- Miyagun ƴan bindiga sun farmaki fadar wani babban basarake a jihar Imo inda suka ƙonata ƙurmus
- Ƴan bindigan dai sun farmaki fadar babban basaraken Ndia Iche Arondizuogu inda banka mata wuta har sai da ta ƙone
- Harin da ƴan bindigan suka kai ya firgita al'ummar ƙauyen inda suka arce zuwa cikin daji suka bar ƙauyen saboda tsoro
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Imo - Ƴan bindiga sun ƙona fadar basaraken Ndia Iche Arondizuogu a ƙaramar hukumar Ideato a jihar Imo, mai martaba Eze Kanu Ikenolu.
Lamarin ya sanya tsoro a zuƙatan mutanen ƙauyen, yayin da suka mutanen ƙauyen ciki har da iyalan basaraken suka arce daga garin.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa ƴan bindigan na isa fadar, suka jefa ababen fashewa a ciki, wanda hakan ya yi sanadiyyar ƙona gidan da motocin da ke a cikin harabarsa.
Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Soye 'Yan Ta'adda Masu Yawa a Arewacin Najeriya a Wani Luguden Wuta Da Suka Yi Musu
Gidan sarautar wanda a cikinsa basaraken yake rayuwa tare da iyalansa, ƴan bindiga sun lalata shi fiye da ƙima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindigan sun ƙona dukiya mai yawa
Shaidun gani da ito sun bayyana cewa kayayyakin miliyoyin naira ne ƴan bindigan suka lalata a gidan, rahoton Tribune ya tabbatar.
Shaidar gani da idon ya bayyana cewa:
"Ƴan bindiga sun farmaki fadar mai martaba Eze Ikenolu, Eze na Ndia Iche Arondizuogu, inda mutanen garin suka arce zuwa cikin daji."
"Har ya zuwa yanzu, babu wani abu da ƴan sanda suka ce dangane da fadar mai martaba Eze Kanu a Ndianiche Arondizuogu, inda aka lalata motoci, gida da kayayyakin miliyoyin naira. Ko Arondizuogu yanzu ba a cikin jihar Imo take ba?
Sai dai, lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin don su fuskanci hukunci.
Jihar Imo ta daɗe tana fama da matsalar ƴan bindiga waɗanɗa suka saba kai hare-hare a fadar sarakunan jihar.
'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Jihar Plateau
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai wani mummunan farmaki a jihar Plateau inda suka halaka mutum biyu har lahira.
Miyagun ƴan bindigan dai sun halaka mutanen ne waɗanda su ke dawowa daga kasuwa a ƙauyen Kinat na ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.
Asali: Legit.ng