"Abun Kunya": Martanin 'Yan Najeriya Bayan Ganin Dakarun Tsaron Da Ke Gadin Tinubu

"Abun Kunya": Martanin 'Yan Najeriya Bayan Ganin Dakarun Tsaron Da Ke Gadin Tinubu

  • Ɗan shugaba Tinubu, Seyi Tinubu ya fito a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta domin murnar ranar matasa ta duniya a wajen shaƙatawa na Jabi Lake Recreational Park a Abuja
  • A wajen, dakarun tsaro na musamman na Special Boat Service (SBS), na rundunar sojin ruwa an nuna su suna ba shi kariya
  • Hotunan da aka watsa a yanar gizo sun fusata ƴan Najeriya kan yadda aka yi wanda ba jami'an gwamnati ba, ake ba shi irin wannan tsaron a wajen da ba shi da wani haɗari

FCT, Abuja - Hotuna sun bayyana a yanar gizo waɗanda suka nuna jami'an tsaron da ke kare lafiyar Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa Bola Tinubu, ɗauke da makamai irin su Israeli IWI Tavor X95s, MEPRO 21, TAR-21 tare da Chinese Type 56-2.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Ya Bayyana Hanya 1 Da Za a Iya Tsige Shugaba Tinubu

Seyi mai shekara 37 a duniya a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, ya garzaya wajen shaƙatawa na Jabi Lake Recreational Park, a Abuja, domin murnar zagayowar ranar matasa ta duniya.

Hotunan Seyi Tinubu sun tayar da kura
'Yan Najeriya sun yi martani bayan ganin hotunan jami'an tsaron Seyi Tinubu Hoto: @Murtalaibin
Asali: Twitter

Ƴan Najeriya sun yi martani bayan ganin dakarun da ke tsaron Seyi

Tambarin da ke a jikin hular ɗaya daga cikin jami'an tsaron da ke tsaron lafiyar ɗan shugaban ƙasar, ya yi kama da tambarin da ke a jikin dakarun musamman na 'Special Boat Service' (SBS), na rundunar sojin ruwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Masu suka sun bayyana cewa Najeriya na da matsala wajen yin amfani da dakarun tsaro yadda yakamata, domin sun kasa fahimtar dalilin da ya sanya dakarun SBS za su bayar da tsaro a wajen da babu wani haɗari sosai.

Dakarun na SBS dai da wuya ake tura su aikin bayar da kariya, har sai dai idan wurin yana da haɗarin gaske.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Gaskiya Ta Fito Kan Makudan Kudaden Da Sanatoci Suka Samu Domin Shakatawa Lokacin Hutu

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin kalaman da aka yi kan hotunan SBS na ba Seyi Tinubu kariya a Twitter.

@oddy4real ya rubuta:

"Ɗa ne a wajen shugaban ƙasa yakamata ya riƙa samun irin wannan tsaron."

@areghan_g ya rubuta:

"Wannan fa duk a cikin kuɗin masu biyan haraji ne! Wata rana ƙila a yi juyin juya hali a Najeriya."

Philips Ndahi ya rubuta:

"Na sha faɗa ba sau ɗaya ba sau biyu ba
Muna buƙatar runduna ta musamman domin bayar da tsaro a fadar shugaban ƙasa (musamman DSS). Sannan idan har wasu tsiraru za su iya samun tsaron PMF da DSS, abun kunya ga dakarun tsaro na musammnan suna bayar da tsaro a wajen da babu haɗari sosai. Akwai takaici."

@sinzubaba ya rubuta:

"Wannan abun kunya ne. Dakarun tsaro na musamman ba an yi su ba ne domin yin gadi ahn ahn."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Mai Laifi Ya Gantsarawa Ɗan Sanda Cizo a Yatsa Lokacin Da Za a Kama Shi

Hotunan Shagalin Bikin Dan El-Rufai Sun Yadu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an gudanar da shagalin Bello Nasir El-Rufai, ɗa a wajen tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Bello El-Rufai dai ya angwance da kyakkyawar amaryarsa Aisha Shu'aibu. Hotunan bikin na su sun ƙayatar sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng