Abba El-Mustapha Ya Bayyana Dalilin Kamen Masu Siyar Da Maganin Gargajiya a Kano
- Hukumar tace finafinai ta ɗab'i ta jihar Kano ta fara kamen masu siyar da magungunan gargajiya a jihar
- Hukumar ta fara gudanar da aikin kamen masu siyar da magungunan ne waɗanda ke amfani da kalaman batsa wajen tallansu
- Shugaban hukumar ya bayyana cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba har sai sun tsaftace jihar daga masu wannan halayyar da ta saɓa wa addinin musulunci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Shugaban hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya yi ƙarin haske kan kamen da hukumar ke yi na masu siyar da magungunan gargajiya.
Al-Mustapha ya bayyana cewa hukumar ta fara kamen ne akan masu siyar da magungunan gargajiyan da su ke amfani kalaman batsa wajen gudanar da tallansu.
Shugaban ya kuma bayyana cewa kamen ya shafi hada masu talla waɗanda suke amfani da hotunan rashin ɗa'a da nufin jan hankulan masi siya wajen tallata magungunansu.
Hukumar ba za ta lamunci rashin ɗa'a ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a Facebook ranar Asabar, Abba ya bayyana cewa shugabancinsa ba zai zuba ido ya bar wannan gurɓatacciyar halayyar ido ta cigaba da faruwa a jihar.
Ya bayyana cewa yin amfani da kalaman batsa ya ci karo da koyarwar addinin Musulunci da tarbiyyar jihar.
Shugaban ya yi wannan jawabin ne a harabar hukumar, jim kaɗan dawowa daga cafke masu siyar da magungunaɓ gargajiyar da suka sa ƙafa suka shure dokar hukumar.
Kamen dai ya gudana ne a wani aikin haɗin gwiwa tsakanin jami'an ƴan sanda da ma'aikatan hukumar.
Abba ya bayyana cew doka ce taba hukumar ikon gudanr da wannan aikin, saboda haka za ta bi dokar sau da ƙafa domin samun nasara.
Gwamnatin Kano Ta Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar.
Gwamnatin a ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da makarantun sun cika dukkanin tsaruka da ƙa'idoji wajen bayar da ingantaccen ilmi a jihar.
Asali: Legit.ng