Obasanjo Ya Yi Kira Da Kiristoci Su Shiga a Dama Da Su a Siyasa
- Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ya koka kan yadda harkar zaɓe ta gurɓace da cin hanci a ƙasar nan
- Obasanjo ya bayyana cewa zaɓe a ƙasar an gina shi ne kan tushe cin hanci wanda hakan ya sanya ba zai haifar da ɗa mai ido ba
- Tsohon shugaban ƙasar ya ɓuƙaci kiristoci da su shiga a dama da su a harkar siyasa domin tsaftace zaɓe a ƙasar nan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa an gurɓata zaɓuka da cin hanci a ƙasar nan inda ya yi kira ga kiristoci da su shiga cikin siyasa domin tsaftace ta, jaridar The Punch ta rahoto.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, a wajen taron yaye ɗalibai na shekara-shekara karo na 57 da cikar shekara 67 na 'The Gospel Faith Mission International' wanda aka gudanar a Gospel City, Ogunmakin akan titin hanyar Legas/Ibadan a jihar Ogun.
Obasanjo, yayin da yake magana akan lakca mai taken 'Rawar da coci za ta taka wajen gina ƙasa a lokaci irin na yanzu', ya bayyana cewa idan akwai rashin tsaro, talauci, yanke burin ci gaba da rayuwa, dole ne coci ta tashi tsaye wajen kawo mafita.
Cin hanci ya yi yawa a zaɓen Najeriya, Obasanjo
"Tushen zaɓe a Najeriya cin hanci ne, sannan ba yadda za ayi cin hanci ya zama tushen wani abun da zai yi kyau." A cewarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da yake bayar da misali da zaɓen shekarar 1999, ya bayyana cewa ya fara shiga halin rashin jindaɗi ne a lokacin zaɓen ƙananan hukumomi lokacin da aka ƙi marawa jam'iyyar PDP baya, rahoton Tribune ya tabbatar.
A kalamansa:
"Halin rashin jindaɗin da na shiga har sau biyu, sun auku ne lokacin da aka yi zaɓen ƙananan hukumomi a shekarar 1999."
"Ƴan kwanaki kaɗan kafin zaɓen, sun tambaye ni ina kuɗin da za a ba ƴan sanda, kuɗin INEC da kuɗin DSS. Na ce babu kuɗi."
Obasanjo ya yi nuni da cewa ya ƙi samar da kuɗaɗen ne saboda yana ganin cewa duk hukumomin gwamnati yakamata a biya su kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukansu.
Obasanjo Ya Fadi Malamin Kiristan Da Zai Shiga Aljanna
A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana malamin addinin kirista ɗaya da zai shiga Aljanna a Najeriya.
Obasanjo ya bayyana cewa Sunday Mbang shi ne shugaban kiristoci a Najeriya da zai shiga aljanna.
Asali: Legit.ng