Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Bayanin Dalilin Da Yasa Farashin Man Fetur Ba Zai Yi Kasa Ba

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Bayanin Dalilin Da Yasa Farashin Man Fetur Ba Zai Yi Kasa Ba

  • Kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya yi ƙarin haske kan dangantakar dake tsakanin matatun man fetur da farashin man fetur
  • Ngelale ya yi bayanin cewa farashin man fetur ya dogara ne akan kuɗin gangar man fetur a kasuwannin duniya
  • Sai dai, Ngelale ya bayyana cewa akwai amfani mai tarin yawa ga ƙasar da take da matatun man fetur masu aiki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Farashin man fetur a gidajen siyar da man fetur ba zai yi ƙasa ba ko da kuwa dukkanin matatun man fetur ɗin ƙasar nan guda biyar suna aiki tare da samar da wadataccen man fetur.

Hakan na ƙunshe ne a cikin kalaman da kakakin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Ajuri Ngelale ya yi ne a wata tattaunawa da gidan talbijin na Television Continental a shirin su mai suna "Your View".

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Jerin Manyan Kasashe 10 Mafi Arhar Man Fetur a Nahiyar Afrika

Farashin man fetur ba zai sauka ba
FG ta yi karin haske kan dangantakar farashin man fetur da matatun man fetur Hoto: State House, Financial Times
Source: UGC

Matatun man fetur masu yawa ba za su sanya farashin man fetur ya sauka ba

A lokacin tattaunawar wacce Legit.ng ta saurara, Ngelale ya yi fatali da batun cewa yawan matatun man fetur zai sanya farashin man fetur ya yi ƙasa, inda ya ce hakan tatsuniya ce kawai domin ba inda hakan ke faruwa a faɗin duniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"Ko da ace muna da matatun man fetur ɗin da su ke samar da man fetur ɗin da ya fi na ko ina a duniya, za ka samu cewa ƙasashen da ke samar da man fetur da matatun man fetur ɗin su...idan ka je ka ga farashin man fetur ɗin su, za ka ga babu bambanci da ƙasashen da ba su da matatun man fetur."

Kakakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa dalilin da ya sanya farashin man fetur ba zai yi ƙasa ba ko da kuwa akwai matatun man fetur shi ne, babu wanda zai kashe biliyoyin kuɗi wajen gina matatun man fetur domin sadaka ko taimakawa al'umma, face sai domin samun riba.

Kara karanta wannan

Kisan Malamin Addinin Musulunci a Gombe: 'Yan Sandan Jihar Sun Fadi Tsauraran Matakan Da Suka Dauka

Farashin Man Fetur Bai Gama Tashi Ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan kasuwa sun hango cewa farashin man fetur bai gama tashi ba a kasuwa.

Ƴan kasuwar sun hango ƙarin tashin farashin man fetur ɗin ne a sakamakon karyewar darajar Naira a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng