Cire Tallafi: Najeriya Ta Shiga Cikin Jerin Kasashe 10 Mafi Arhar Man Fetur A Afrika
- Najeriya ta shiga cikin jerin ƙasashen Afrika 10 da suka fi ko ina shan man fetur da arha
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar IPMAN ta koka kan yiwuwar ƙaruwar farashin mai a ƙasar
- Najeriya na fuskantar hauhawar farashin fetur sakamakon karyewar darajar naira da ake ƙara samu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Biyo bayan karyewar darajar naira da aka samu, kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ta yi gargaɗin cewa za a iya samun ƙaruwar farashin man fetur.
Legit.ng ta yi rahoto kan yadda darajar naira ta ƙara karewa zuwa N930 a kan duk dalar Amurka ɗaya a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta.
Dilallai sun yi magana kan yiwuwar ƙaruwar farashin man fetur
Kungiyar dilallan man fetur mai zaman kanta ta ƙasa wato IPMAN, ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun sauye-sauye a farashin man fetur da ake sha a Najeriya.
Da Dumi-Dumi: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Yi, Sun Bayyana Ranar Dawowa Bakin Aiki
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai a zantawarsa da Legit.ng, shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa Chinedu Okoronkwo, ya ce kar 'yan Najeriya su samu damuwa dangane da hakan.
Duk da sauye-sauyen da aka samu a harkar kasuwancin man fetur, ciki kuwa har da bai wa ƙarin 'yan kasuwa damar shiga cikin harkar dumu-dumu, Najeriya ta kasance ta shida cikin jerin ƙasashen Afrika 10 da suka fi shan mai da arha.
Ƙasashen Afrika 10 mafi arhar man fetur
Wani rahoto da shafin Global Petrol Prices ya wallafa, ya nuna jerin ƙasashen duniya da kuma farashin yadda suke shan man fetur.
Duk da halin karyewar darajar naira da Najeriya ta tsinci kanta a ciki, ta yadda ake sayar da dala akan naira 770 a gwamnatance, ƙasar ta na shan man fetur a kan dala 0.822 (kwatankwacin naira 632) a duk lita.
Rahoton ya lissafo ƙasashe 10 na Najeriya, da kuma farashin da suke shan man fetur a kai.
1. Libya - dala 0.031
2. Algeria - dala 0.338
3. Angola - dala 0.364
4. Egypt - dala 0.372
5. Tunisia - dala 0.817
6. Nigeria - dala 0.822
7. Liberia - dala 0.937
8. Sudan - dala 0.992
9. Gabon - dala 1.011
10. Botswana - dala 1.073
Dillalan man fetur sun hango yiwuwar tashin farashin man fetur
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hangen da ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ta yi na yiwuwar samun ƙarin farashin man cikin 'yan kwanakin nan.
Kungiyar dilallan ta ce karyewar darajar naira ce za ta janyo ƙaruwar farashin, inda ta nemi shugaba Bola Tinubu da ya yi ƙoƙarin ganin ya ɗaga darajar naira.
Asali: Legit.ng