Kungiyar AU Ta Goyi Bayan ECOWAS Kan Daukar Matakin Soji A Kan Jamhuriyar Nijar

Kungiyar AU Ta Goyi Bayan ECOWAS Kan Daukar Matakin Soji A Kan Jamhuriyar Nijar

  • Kungiyar Tarayyar Nahiyar Afirka, AU ta goyi bayan matakin da kungiyar ECOWAS ga dauka na tura dakaru Nijar
  • Shugaban kungiyar, Moussa Faki Mahamat shi ya bayyana haka inda ya ce a shirye suke don taimakawa ECOWAS
  • Kungiyar ECOWAS a wata ganawa a birnin Abuja ta umarci dakarunta da su daura damarar yaki a Jamhuriyar Nijar

Yamai, Nijar - Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta ci alwashin taimakawa Kungiyar ECOWAS kan matakin soji a Jamhuriyar Nijar.

Shugaban kungiyar, Moussa Faki Mahamat shi ya bayyana haka inda ya ce suna goyon bayan matakin na ECOWAS.

Kunfiyar AU ta goyi bayan ECOWAS kan daukar matakin soji
Kungiyar Tarayyar Afirka, AU Ta Bayyana Ra'ayinta Kan Matakin Soji A Nijar. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Meye AU ta ce kan matakin ECOWAS?

Mahamat ya gargadi sojin Nijar da su saki hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum da iyalansa, Daily Nigerian ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Jerin Kasashe 6 Na Afirka Ta Yamma Da ECOWAS Ta Afkawa A Nahiyar, Bayanai Sun Fito

A cewarsa:

"Yadda ake rike da shugaban farar hula a wannan hali bai dace ba.
"Bazoum na cikin wani irin yanayi mummuna wanda ba za mu amince da shi ba."

Sojin Jamhuriyar Nijar sun kifar da Mohamed Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yuli tare da rusa dukkan hukumomin gwamnati da kuma kundin tsarin mulki.

Barazanar meye ECOWAS ta yi ga Nijar?

Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta yi kakkausar suka a kan juyin mulkin da aka yi inda ta gargadi sojin da su mika mulki ga Mohamed Bazoum cikin ruwan sanyi.

Sojin sunyi fatali da umarnin kungiyar ECOWAS inda daga bisa kungiyar ta saka wasu takunkumi ga kasar a kokarin tilasta musu mika mulkin.

Yayin wata ganawa da kungiyar ECOWAS din ta yi a Abuja, kungiyar ta umarci dakarunta su tsaya a kan shiri don daukar mataki.

A martanisu, sojin juyin mulki na Nijar sun yi barazanar kashe Shugaba Bazoum idan kungiyar ECOWAS ta kawo hari Nijar, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: ECOWAS Ta Umurci Sojojinta Su Ɗaura Ɗamarar Yaƙar Sojojin Nijar, Bayanai Sun Fito

Sojojin Nijar Sun Kafa Sabuwar Gwamnati

A wani labarin, sojojin juyin mulkin Nijar sun kafa sabuwar gwamnati mai dauke da ministoci 21 don tabbatar da ikonsu a kasar.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ECOWAS ta yi wa sojojin barazanar daukar matakin soji kan kasar bayan hambarar da Mohamed Bazoum.

Sojijin sun yi fatali da barazanar na kungiyar ECOWAS tare da yin gargadin kashe Bazoum idan har kungiyar ta turo dakarunta kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.