An Bukaci Sanatoci Su Bayyana Bayanan Asusun Bankin su Yayin Da Tsohon Jigon APC Ya Fallasa Kudin Da Aka Ba Su
- An buƙaci sanatoci da ƴan majalisar wakilai na tarayyar Najeriya su wallafa bayanan asusun ajiyar su na banki
- Kwamared Timi Frank, tsohon kakakin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), shi ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta
- Ya bayyana cewa sanatoci sun samu N30m, shugabannin majalisa sun samu N45m a matsayin kuɗin shaƙatawa lokacin hutu
FCT, Abuja - Tsohon kakakin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Kwamared Timi Frank, ya ƙalubalanci ƴan majalisa da su wallafa bayanan asusun ajiyarsu na banki.
Kwamared Frank ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan kalaman shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, a lokacin zaman majalisa inda ya ce an tura musu kuɗi domin su ji daɗin hutun su.
A cikin wata sanarwa da ya fita ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, a birnin tarayya Abuja, Frank ya buƙaci ƴan majalisar da su mayar da kuɗaɗen da aka tura musu, cewar rahoton Blueprint.
Timi Frank ya fallasa miliyoyin da aka tura wa sanatoci
Kamar yadda yake ƙunshe a cikin sanarwar, Frank ya bayyana cewa kowane sanata ya samu N35m yayin da shugabannin majalisar suka samu N50m.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar rahoton Nigerian Tribune, ya bayyana cewa:
"A cewar wani sanata daga yankin Arewa maso Yamma wanda ya gaya min gaskiya, kowane sanata ya samu N35m yayin da shugabannin majalisar suka samu N45 kowanen su."
"Ya kuma gaya min cewa kowane ɗan majalisar wakilai ya samu N30m yayin da shugabannin majalisar suka samu N45m."
Timi Frank ya bayyana cewa ya sami bayanansa ne daga wajen majiya mai tushe, wani sanata a majalisar dattawa.
A kalamansa:
"Sanatan ya bayyana cewa bai ƙarbi kuɗin ba, inda yace Allah ba zai yafe masa ba idan ya karɓi waɗannan maƙudan kuɗaɗen domin ya ji daɗi a lokacin hutu, yayin da waɗanda yake wakilta ke shan wuya. Ya ce babu inda zai je saboda haka bai buƙatar kuɗin.
An Maka Akpabio Kara a Kotu
A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ƙara a gaban kotu, saboda kuɗin da aka ba sanatoci domin shaƙatawa a lokacin hutu.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da abin da sanatocin suƙa yi a daidai lokacin da miliyoyin ƴan Najeriya ke cikin halin matsin rayuwa.
Asali: Legit.ng