Wani Da Ake Zargi Da Aikata Kisa Ya Gantsarawa Dan Sanda Cizo a Ogun

Wani Da Ake Zargi Da Aikata Kisa Ya Gantsarawa Dan Sanda Cizo a Ogun

  • Jami'an 'yan sandan jihar Ogun, sun kama wasu mutane uku bisa zargin aikata miyagun laifuka
  • 'Yan sandan sun kama mutanen da ake zargi da aikata kisan kai yayin da suke tuƙa wani babur mara lamba
  • A ƙoƙarinsa na ganin ya tsere daga hannun jami'an, ɗaya daga cikinsu ya gantsarawa ɗan sanda cizo

Jihar Ogun - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da aikata kisan kai tare da wani fasinja ɗaya.

An kama mutanen da ake zargin ne a ranar Lahadi, a kan titin Papalanto da ke hanyar Legas zuwa Abeokuta kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola ce ta tabbatarwa da manema labarai batun kama waɗanda ake zargin a Abeokuta ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Mutane 17

'Yan sanda sun kama mutane 3 bisa zargin kisan kai
Mai kaifi ya gantsarawa ɗan sanda cizo a yatsa. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama waɗanda ake zargi

Odutola ta ce an samu mutanen da ake zargi, Esube da wani mai suna Osunmuyiwa Solomon, tare da wata ƙaramar bindiga ƙirar cikin gida cike da harsashi a lokacin da aka kama su.

Ta ƙara da cewa, an kama mutanen ne bayan da Esube ya bayyana cewa dukkansu suna da hannu wajen kashe-kashe a yankinsu.

A cewar Odutola, tawagar 'yan sanda da ke sintiri a kan hanya ƙarƙashin jagorancin Insifekta Sunday Adeyemo, sun yi ƙoƙarin tsayar da ƙasurguman masu laifin a yayin da suka zo wucewa a kan babur mara lamba.

Ta ce mutanen sun ƙi tsayawa, inda suka yi ƙoƙarin guduwa, wanda daga nan ne aka bi su kuma aka kamo su tare da wani fasinja guda ɗaya.

Ya gantsarawa ɗan sanda cizo domin ya tsere

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Mary Odili Tana Aiki Domin Tinubu Ya Samu Nasara? Gaskiya Ta Bayyana

Odutola ta kuma ƙara da cewa, a ƙoƙarin ganin ya arce a yayin kamen, Esube ya gantsatarawa ɗan sanda cizo a yatsansa.

Ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da mutanen a gaban kotu bisa zargin kisan kai, sata da kuma mallakar makamai.

A rahoton Daily Post, ɗaya daga cikin mutanen ya shaidawa jami'an tsaro cewa babur ɗin da aka kama su da shi na sata ne.

An kama mutane 6 bisa zargin fashi da makami a Bauchi

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wasu mutane shida da jami'an 'yan sandan jihar Bauchi suka kama bisa zargin fashi da makami.

'Yan sandan sun yi nasarar kamo mutanen ne a yayin da suka fita wani rangadi, inda suka cimma musu a ɗaya daga cikin maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng