Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Rabon Tallafi Ga Talakawa Da Masu Kananan Sana'o'i
- Gwamnatin jihar Jugawa ta shirya rabon tallafi ga talakawa masu ƙaramin ƙarfi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
- Gwamnatin jihar za ta kuma tallafawa masu ƙananan sana'o'i da jarin da za su ƙara domin bunƙasa sana'o'in su
- Tsarin rabon tallafin na gwamnatin dai zai gudana ne a gaba ɗaya ƙananan hukumomin jihar guda 27
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta shirya rabon tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ga al'ummar jihar ciki har da masu ƙananan sana'o'i.
Kwamishinan watsa labarai, matasa da wasanni da al'adu, Sagir Musa, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Facebook, kan abubuwan da majalisar zartaswar jihar ta cimmmawa a taron su a birnin Dutse.

Source: Facebook
Musa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da fitar da N134m domin siyo tirelolin shinkafa guda biyar domin raba wa masu ƙaramin ƙarfi.

Kara karanta wannan
Sauƙi Ya Zo: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Bayyana Mafi Karancin Albashin da Zata Ƙara Wa Ma'aikata a Najeriya
Su wanene za su amfana da tallafin?
Kwamishinan ya ƙara da cewa majalisar ta amince da shirin tallafi ga matasa masu sana'o'i 1,500 a cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa kowane daga cikin su zai amfana da N50,000 domin ƙara ƙarfin jari a kasuwancin su.
Musa ya bayyana cewa shirin zai gudana ne a ƙarƙashin ma'aikatar watsa labarai, matasa, wasanni da al'ada tare da haɗin gwiwa da hukumar samar da ayyukan yi da dogaro ga kai ta jihar.
Ya kuma ƙara da cewa majalisar ta amince da bayar da tallafin N100,000 ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa 1,000 ta hanyar shirin 'J-Cares' wanda babban bankin duniya yake bayar da tallafi a kai.
Sai dai, kwamishinan ya bayyana cewa masu ƙananan sana'o'in da suka cika sharuɗɗan bankin duniya na samun asusun ajiya, lambar BVN da aƙalla ma'aikata biyu a ƙarƙashin su ne za su amfana da tallafin.

Kara karanta wannan
Sunayen Ministoci: Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu
Jama'a sun yaba da tallafin
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu mazauna birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, waɗanda suka nuna farin cikin su kan wannan tsarin tallafin da gwamnan ya zo da shi.
Ɗaya daga cikin su mai suna Malam Anas ya bayyana cewa lallai wannan tsarin ba ƙaramin taimakawa zai yi ba, musamman ga matasa masu ƙananan sana'o'i.
Malam Shamsu kuwa nuna ƙwarin gwiwarsa ya yi akan gwamnan, inda ya ce mai faɗa da cika wa ne, ya san cewa tun da aka ce za a bayar da tallafin to lallai za a bayar, ba surutu ba ne kawai irin na ƴan siyasa.
Gwamnan Jigawa Ya Yi Kira Ga 'Yan Najeriya
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya yi muhimmin kira ga ƴan Najeriya kan gwamnatin Shugaba Tinubu.
Gwamnan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da wahalhalun da su ke sha a mulkin na Tinubu, domin sauƙi yana nan zuwa nan ba da daɗewa ba.
Asali: Legit.ng