Bayan Ganawa Da Shugabannin Juyin Mulkin Nijar, Sanusi Na Kus-Kus Da Tinubu

Bayan Ganawa Da Shugabannin Juyin Mulkin Nijar, Sanusi Na Kus-Kus Da Tinubu

  • Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi na ganawar sirri da shugaban kasa Bola Tinubu
  • Koda dai babu cikakken bayani kan ganawar da ya gudana a Abuja, amma ana ganin ba zai rasa nasaba da ganawar da Sanusi ya yi da gwamnatin mulkin sojan Nijar
  • Ganawar Sanusi ya zo ne bayan da gwamnatin mulkin soja ta ki amincewa da wani taron da aka shirya yi da wakilan kungiyar AU, ECOWAS, da jami’an diflomasiyya na Amurka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mai martaba Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi suna cikin wata ganawa ta sirri yanzu haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Juyin mulki: Sanusi da Tinubu sun yi ganawar sirri

Sanusi da Tinubu sun gana bayan ya dawo daga Nijar
Yanzu Yanzu: Bayan Ganawa Da Shugabannin Juyin Mulkin Nijar, Sanusi Na Kus-Kus Da Tinubu Hoto: @BMB1_Official
Asali: Facebook

Bayanai kan ganawar Sanudi da Tinubu

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

A baya-bayan nan ne Sanusi ya dawo daga Jamhuriyar Nijar inda ya je ganawa da shugabannin juyin mulki wadanda suka kwace mulki daga hannun zababben shugaban kasa Muhamed Bazoum.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanusi Lamido Sanusi ya isa fadar shugaban kasa da misalin 8:25 na dare jim kadan bayan tawagar kungiyar Malaman Najeriya sun gana da shugaban kasar, rahoton Vanguard.

Da aka tambaye shi game da ziyarar da ya kai Jamhuriyar Nijar, tsohon Sarkin ya ce, lafiya kalau.

Har a daidai lokacin kawo wannan rahoton, Sanusi na cikin ganawa da shugaban kasar.

Gwamnatin sojan Nijar ta ki ganawa da wakilan Amurka

Wannan ganawar na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin kasar ta ki amincewa da wani taron da aka shirya yi da wakilan kungiyar Tarayyar Afirka (AU), kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), da kuma jami'an diflomasiyya na Amurka, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Zauna Da Sojojin Da Suka Kifar Da Bazoum a Nijar

Hankalin duniya gaba daya ya karkata kan Nijar bayan juyin mulki da aka yi a kasar wanda ya girgiza yankin a yan kwanakin nan.

Dakarun tsaron kasar, da ya kamata su kare zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, sun tare fadar shugaban kasar.

Juyin Mulkin Nijar: Sarkin Musulmi Ya Yi Watsi Da Takunkumin ECOWAS Da Tsoma Bakin Sojoji

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa majalisar Koli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bayyana matsayinta dangane da takunkumin da kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta kakaba ma jamhuriyar Nijar.

A ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, mataimakin babban sakataren NSCIA, Salisu Shehu, ya ce majalisar ta yi adawa da takunkumin da ECOWAS ta kakabawa Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli a kasar ta yammacin Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng