Babban Fasto Ya Hango Wani Gagarumin Abu Na Tunkaro Najeriya, Ya Gargadi Shugabanni

Babban Fasto Ya Hango Wani Gagarumin Abu Na Tunkaro Najeriya, Ya Gargadi Shugabanni

  • Iginla ya bayyana cewa ya hango wani babban abu kamar girgizar ƙasa na tunkaro ƙasar nan, wanda shugabanni masu gaskiya ne kawai za su tsira idan ta zo
  • Iginla ya buƙaci shugabannin da su kasance masu gaskiya da riƙon amana da samar wa waɗanda suka shugabanta romon dimokuraɗiyya
  • Babban faston ya kuma gargaɗi Shugaba Tinubu da ya yi taka tsantsan kan mayar da abokansa zuwa maƙiyansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Fasto Joshua Iginla, shugaban cocin Champions Royal Assembly, ya gargaɗi shugabanni a Najeriya kan yi wa jama'a ƙarairayi, inda ya bayyana cewa ya hango cewa nan ba da daɗewa ba mutane za su yi musu zanga-zanga.

A cikin wani bidiyon wa'azi da aka sanya a shafin Youtube na cocin, Iginla ya bayyana cewa ya hango wani abu kamar girgizar ƙasa na zuwa Najeriya sannan shugabanni masu niyyar gaskiya ne kawai za su tsira.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Fasto Iginla ya yi sabon hasashe
Fasto Iginla ya yi sabon hasashe kan Tinubu da sauran shugabanni Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Fasto Iginla ya gargaɗi Shugaba Tinubu

Fasto ya buƙaci Shugaba Tinubu da ka da ya mayar da abokansa su zama maƙiyansa ko maƙiyansa su zama abokansa da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Dole ne shugabannin mu su yi taka tsan-tsan wajen ba mutane romon dimokuraɗiyya. Na hango wani abu kamar girgizar ƙasa na zuwa Najeriya. Shugabanni masu gaskiya ne kaɗai za su tsira."
"Kamar tunzura ce wacce za ta fusata matasa. Idan akwai abin da shugabannin mu yakamata su yi, su gaggauta yin hakan. Allah ya taimake mu."

Fasto Iginla ya buƙaci shugabanni su yi gaskiya

Iginla ya buƙaci shugabanni da su yi gaskiya sannan su tabbatar waɗanda su ke shugabanta sun amfana da romon dimokuraɗiyya.

Idan ba a manta ba dai, fasto Iginla ya hango nasarar Shugaba Tinubu kafin zuwan lokacin zaɓen fidda gwanin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Hukumar Kwastam Ta Yi Bayani Kan Dalilin Rufe Iyakokin Najeriya Da Nijar

Ayodele Ya Yi Sabon Hasashe

A wani labarin kuma, babban fasto Primte Elijah Ayodele, ya hango wani mummunan abu da zai faru a mulkin Tinubu.

Ayodele ya bayyana cewa rigima za ta ɓarke a tsakanin wasu daga cikin ƴan siyasar da aka zaɓa tare da iyayen gidansu a siyasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng