Babu Najeriya Ciki: Seychelles Ce Kan Gaba a Jerin Kasashe 10 Mafi Arzikin 'Yan Kasa a Afirka a 2023
- Bankin duniya ya fitar da jerin kasashen Afrika 10 mafi arziƙi ta la'akari da abinda mutum ɗaya ke iya samu
- Masana tattalin arziƙi na kasafta tarin dukiyar ƙasa da yawan mutanen cikinta domin gane yanayin ci gabanta
- Duk da kasancewar Najeriya mafi tarin dukiya a Afrika, ba ta samu shiga cikin jerin ƙasashen da mutanenta suka fi arziki ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Nahiyar Afrika mai ɗauke da ƙasashe 54, ta kasance ita ce ke da kashi 25% na yawan al'ummar duniya.
Afrika na da masu kuɗi da ke tasowa waɗanda daga cikinsu akwai waɗanda ake gogayya da su a duniya.
Duk da yawan jama'a da suka kai aƙalla biliyan 1.2 da kuma tarin albarkatun ƙasa da nahiyar ke da su, babu jin daɗin rayuwa kamar yadda 'yan wasu nahiyoyin ke ji.
Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Matakin da aka bi wajen zakulo ƙasashen Afrika 10 mafi arziƙi
A cikin wani rahoto da bankin duniya ya haɗa, an bayyana cewa ƙasar Seychelles, wacce ke da yawan jama'a da aka ƙiyasta su a 100,600, ita ce ta fi kowace ƙasa a Afrika arziki a shekarar 2023.
An yi duba ya zuwa 'GDP Per Capita', ma'ana an raba tarin dukiyar da ƙasa ke da ita da yawan al'ummar da take da su, wanda hakan zai ba da kason da kowa zai iya samu.
Kasar Mauritius ce ke takewa Seychelles baya, yayin da ƙasar Libya ta zo ta uku duk kuwa da irin ƙalubalen da take fuskanta.
Rahoton ya tattaro cewa ƙasar Madagascar, Nijar da Burundi ne ke can ƙasa a jerin ƙasashen na Afrika mafi arziƙi.
Duk da yawan kuɗaɗen da Najeriya ke samu, wanda ya zarce na kowace ƙasa a Afrika kamar yadda yake a Statista, ita ce ta 25 a cikin jerin ƙasashen Afrika mafi arziƙi.
Ƙasashen Afrika 10 da suka fi arziƙi a duk mutum 1
Ƙasashe | Kiyasin arziƙin mutum |
Seychelles | $35,227 |
Mauritius | $26,905 |
Libya | $26,905 |
Botswana | $18,323 |
Equatorial Guinea | $17,396 |
Afrika ta Kudu | $15,904 |
Algeria | $13,209 |
Tunisia | $12,489 |
Namibia | $11,205 |
Eswatini | $10,782 |
Kuɗaɗen kasashe 10 mafi rauni a Afrika
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan kuɗaɗen ƙasashe 10 mafi rauni a Afrika yayin da kowace ƙasa ke fafutukar ganin ta ɗaga darajar kuɗaɗenta.
Kuɗaɗen Najeriya, wato naira, ba su cikin kuɗaɗe mafiya rauni a nahiyar ta Afrika.
Asali: Legit.ng