An Shiga Jimami Bayan Fasto Taiwo Odukoya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Jimami Bayan Fasto Taiwo Odukoya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An yi rashin babban fasto wanda ya assasa cocin 'The Fountain of Life Church' wacce ke a Ilupeju cikin jihar Legas
  • Fasto Daniel Taiwo Odukoya ya yi bankwana ds duniya yana da shekara 67 s wani asibiti a ƙasar Amurka
  • Cocin ita ce ta tabbatar da mutuwar babban faston wanda haifaffen jihar Kaduna ne a cikin wata sanarwa

Jihar Legas - Fasto Taiwo Odukoya, babban fasto a cocin 'The Fountain of Life Church', ya riga mu gidan gaskiya.

An tabbatar da mutuwar faston ne a shafin Facebook na cocin a ranar Talata, 8 ga watan Agusta.

Fasto Taiwo Odukoya ya mutu
Faston ya mutu yana shekara 67 Hoto: The Fountain of Life Church
Asali: Facebook

Malamin addinin ya yi bankwana da duniya ne a wani asibiti a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta a ƙasar Amurka.

Sanarwar na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

"A bisa miƙa komai zuwa ga ubangiji, cocin 'The fountain of Life Church' na sanar da mutuwar jagora, malami kuma bawan Allah, fasto Daniel Taiwo Odukoya, wanda ya kafa cocin 'The Fountain of Life Church', wanda ya bar duniya a ranar 7 ga watan Agustan 2023 a ƙasar Amurka."

Wanene fasto Taiwo Odukoya?

Odukoya, wanda ya mutu yana da shekara 67, an haife shi ne a jihar Kaduna dake yankin Arewa maso Yamma.

Cocin 'The Fountain of Life Church' wacce ke a Ilupeju cikin jihar Legas wacce shi ne babban fastonta, tana da mambobi sama da mutum 8,000.

Fasto Odukoya ya yi karatun firamarensa da na sakandire a makarantar firamaren Baptist a hanyar Kigo a Kaduna da kwalejin St. Paul's College, wacce ake kira da Kufena College, dake a Wusasa, cikin birnin Zaria a jihar Kaduna.

A shekarar 1976, Odukoya ya wuce jami'ar Ibadan, inda a shekarar 1981 ya samu digiri a fannin injiniyan man fetur.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Sake Sanya Labule Da Farfesa Okonjo-Iweala, Bayanai Sun Bayyana

Bayan ya kammala hidimtawa ƙasa (NYSC) a shekarar 1982, Odukoya ya fara aiki da kamfanin man fetur na ƙasa inda ya yi aiki har zuwa lokacin da ajiye aiki domin ƙashin kansa a watan Janairun 1994, sannan ya kama harkokin coci.

Babban Faston RCCG Ya Mutu

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ya yi bankwana da duniya.

Farfesa Folagabade Aboaba ya mutu ne yana da shekara 90 a duniya bayan ya yi fama ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng