Mata Ta Garzaya Kotu Tana Neman Saki Saboda Mijinta Baya Iya Ciyar Da Ita

Mata Ta Garzaya Kotu Tana Neman Saki Saboda Mijinta Baya Iya Ciyar Da Ita

  • Wata matar aure ta shigar da mijinta ƙara gaban kotu tana mai neman a raba aurensu
  • Matar mai suna Roima, ta koka kan yadda mijinta Ahmed ke gaza ciyar da ita yadda ya dace
  • Sai dai a na sa ɓangaren, mijin ya ce halin tsadar rayuwar da ake ciki ne ya sanya ba ya iya sauke nauyin da ke kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ilorin, jihar Kwara - Wata mata mai suna Roima Abdulkadir, ta nemi wata kotu da ke cikin birnin Ilorin, da ta raba aurenta da mijinta Ahmed Abdulkadir.

Ta ce tana son rabuwa da mijin ne saboda gazawarsa wajen ciyar da ita da kuma rashin ba ta kuɗaɗen da za ta kula da kanta kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mata ta kai ƙarar miji kotu kan matsalar abinci
Mata ta nemi mijinta ya saketa saboda ya gaza ciyar da ita. Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Mijin ya nemi kotu da ta ba shi lokaci don samun daidaito da matar ta sa

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

Sai dai a na sa ɓangaren, Ahmed Abdulkadir ya nemi kotun da ta ba shi lokaci domin ya shawo kan matar ta sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ahmed ya ce ba ya son rabuwa da matar ta sa saboda matuƙar ƙaunarta da yake yi.

Ya ce shi ƙwararren tela ne kuma yana jan babur mai ƙafa uku, amma duk da haka ba ya iya samun kuɗaɗen da zai biyawa iyalinsa buƙatunsu saboda halin rashin kuɗin da ake ciki.

Alƙali ya bai wa mijin damar sulhuntawa da matar ta sa

Mai shari'a AbdulQadir Umar, ya bai wa Ahmed damar zuwa domin ya sulhuntawa da matar ta sa.

Ya ce a koda yaushe kotu na marhabun da sulhu a tsakanin waɗanda suka samu saɓani.

Ya shawarci wanda ake ƙara da ya yi ƙoƙari wajen bai wa matar ta sa kulawar da ta dace da ɗan abinda yake samu a kowace rana.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

Daga ƙarshe, alƙalin ya ɗage sauraron shari'ar zuwa 5 ga watan Satumba domin jin yadda sulhun ya kaya kamar yadda ya zo a rahoton na Daily Trust.

Tun bayan cire tallafin man fetur abubuwa suka taɓarɓare a Najeriya. Sai dai wasu gwamnoni na bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun ragewa 'yan jihohinsu raɗaɗin da suke ciki.

Miji ya ce matarsa da mahaifiyarta sun haɗa baki don su kwashe masa dukiya

Legit.ng a baya ta kawo rahoton wani ma'aikacin banki da ya koka kan yadda matarsa da mahaifiyarta suka haɗa baki suke tatsar kuɗaɗe daga aljihunsa.

Ya ce a duk lokacin da matar ta je kasuwa domin sayo kayayyakin amfani na gida, takan zambaɗa kuɗaɗen har ma su wuce tunani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng