Sanatan APC Ya Koka Bayan 'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Hadiminsa

Sanatan APC Ya Koka Bayan 'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Hadiminsa

  • Sanata Solomon Adeola ya yi magana kan mutuwar ɗaya daga cikin hadimansa, Olaniyi Sanni wanda ƴan bindiga suka halaka
  • Sanatan mai wakiltar Ogun ta Yamma, wanda ya nuna godiyarsa bisa saƙonnin ta'aziyyar da ya samu, ya haƙiƙance lallai sai an gano waɗanda suka halaka Olaniyi
  • Sanatan ya halarci zaman majalisar dattawa na ranar Litinin inda aka kammala tantancewa da tabbatar da ministoci 45 cikin 48

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abeokuta, jihar Ogun - Sanatan dake wakiltar Ogun ta Yamma, Solomon Adeola, ya fitar da sanarwa kan mutuwar wani jajirtaccen hadiminsa.

Bayan ya halarci zaman majalisar dattawa na ranar Litinin, 7 ga watan Agusta, inda aka tantance da tabbatar ministoci 45 cikin 48, Adeola ya yi martani kan mutuwar Olaniyi Sanni, wanda aka halaka a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

An Samu Hargitsi a Majalisar Dattawa Wajen Tantance Ministan Tinubu, Bayanai Sun Fito

Sanata Adeola ya magantu kan kisan hadiminsa
Sanata Adeola ya hakikance dole sai an gano makasan hadiminsa Hoto: Senator Solomon Olamilekan Adeola, FCA
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya sanya a shafinsa na Facebook, Adeola ya yi jimamin rasuwar Sanni wanda ya bayyana a matsayin hadimi mai biyayya.

Sanata Adeola ya yi magana mai kaushi

Sanatan wanda shine shugaban kwamitin kasafin kuɗi, ya nuna godiyarsa ga ƴan Najeriya bisa ta'aziyyar da suka yi masa sannan ya buƙaci dole sai an gano makasan da suka halaka babban hadiminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nuna godiyarsa ga takwarorinsa waɗanda suka ta ya shi jimamin rasuwar Sanni.

Rubutun na sa wanda Legit.ng ta ci karo da shi a ranar Talata, 8 ga watan Agusta, na cewa:

"Cikin baƙin ciki da jimamin rasuwar jajirtaccen hadimi, na iso majalisa domin tantancewa da tabbatar da ministocin da aka naɗa."
"Na samu ta'aziyya daga shugaban masu rinjaye na majalisa, Sanata Opeyemi Bamidele, Sanata Tokunbo Abiru, Sanata Francis Fadahunsi, Sanata Tony Nwoye da Barr. Festus Keyamo, ministan da aka naɗa."

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

"Na yaba sosai da saƙonnin ta'aziyyar da na samu daga wajen ƴan Najeriya daga ko wani ɓangare. Komai zai yi mana daidai amma dole sai an gano makasan hadimina."

DSS Ta Titsiye Sakataren Gwamnatin Ogun

A wani labarin kuma, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta titsiye sakataren gwamnatin jihar Ogun bisa wasu zarge-zarge.

Hukumar na tuhumar Tokunbo Talabi da hannu wajen buga takardun zaɓe na 2023 da badaƙalar kuɗaɗen Covid-19.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng