Manomi Ya Yi Nasarar Halaka Shugaban 'Yan Ta'addan Da Ya Kashe Masa 'Ya'ya 3 a Kaduna

Manomi Ya Yi Nasarar Halaka Shugaban 'Yan Ta'addan Da Ya Kashe Masa 'Ya'ya 3 a Kaduna

  • Manomi ya yi jarumta inda ya halaka ƙasurgumin ɗan ta'addan da ya addabi ƙauyensu
  • Manomin ya kama shugaban ɓarayin da kokawa, inda a cikin hakan ne ya yi sa'ar aika shi barzahu
  • Shugaban ɓarayin da aka bayyana sunansa da Wizi, shi ne ya kashe 'ya'yan manomin guda uku a can baya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - Wani manomi da ba a bayyana sunansa ba, ya yi fito na fito da wasu 'yan ta'adda da suka kawo masa farmaki a gonarsa, inda ya yi nasarar halaka shugabansu.

Lamarin ya faru ne a lokacin da 'yan ta'addan suka dawo domin tafiya da manomin, wanda suka kashewa 'ya'ya uku a kwanakin baya kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Manomi ya kashe shugaban barayi a Kaduna
Manomi ya yi jarumta, ya kashe shugaban 'yan bindiga a Kaduna. Hoto: KDSG
Asali: UGC

Manomin da ɗansa sun yi wa 'yan ta'addan turjiya

An bayyana cewa manomin da ɗansa da suke aiki a gonarsu, sun ƙi amincewa su bi ɓarayin a lokacin da suka nemi tafiya da su.

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana cikin haka ne faɗa ya kaure tsakaninsu, inda shugaban ɓarayin ya umarci ɗaya daga cikin mutanensa da ya harbi mutumin.

Sai harsashin da aka harba ya kuskure manomin inda ya kauce ya je ya samu ɗan nasa a ƙafa.

Manomin ya kama shugaban 'yan ta'addan da kokawa

Wani shugaban al'umma a yankin, ya ce a lokacin da yaron ya faɗi ƙasa ciki jini, sai shugaban 'yan ta'addan mai suna Wizi, ya yi ƙoƙarin caka masa wuƙa.

Ya ce a ƙoƙarin manomin na ganin ya ceci rayuwar ɗan nasa, sai ya kama Wizi da kokawa inda a cikin hakan ya yi nasarar ƙwace bindigar da ke hannunsa, inda take ya ɗura masa albarusai.

Ya ƙara da cewa ganin abinda ya faru ne ya sanya sauran 'yan ta'addan suka ranta a na kare zuwa cikin jeji kamar yadda ya zo a rahoton na Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau Ya Bukaci Iyaye Su Tura Yara Mata Koyon Aikin Likitanci, Ya Ba Da Dalili

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke yawan fama da hare-haren 'yan bindiga akan manoma da sauran jama'ar gari baki ɗaya.

Yan bidniga sun kashe wani babban malamin izala Kaduna

A baya, Legit.ng ta yi rahoto kan wani babban malami na ƙungiyar Izala da 'yan ta'adda suka kashe a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

'Yan ta'addan sun kuma yi nasarar tafiya da manoma aƙalla 40 a ƙakuyukan da mummunar lamarin ya faru.

'Yan bindiga sun sace mutane 7 tare da kashe manomi a Kaduna

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sace wasu mutane bakwai da 'yan bindiga suka yi a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna.

Haka nan 'yan bindigar sun kuma kashe wani manomi a ƙauyen da suka aiwatar da wannan ɗanyen aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng