Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'addan Boko Haram 11 a Jihar Borno
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴam ta'addan Boko Haram masu a dajin Sambisa na jihar Borno
- Sojojin sun halaka ƴan ta'adda 11 tare da lalata maɓoyarsu a wurare masu yawa a cikin dajin na Sambisa
- Dakarun sojojin sun kuma cafke wasu ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai da sauran kayayyakin aiki a hannun su
Jihar Borno - Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadin Kai' tare da haɗin gwiwar ƴan sakai (CJTF) sun halaka mayaƙan Boko Haram a dajin Sambisa.
Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda 11 tare da cafke wasu huɗu da ransu a dajin Sambisa cikin jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne a tsakanin ranakun 4 da 5 na watan Agusta lokacin da suka kutsa cikin maɓoyar ƴan ta'addan a dajin Sambisa cikin ƙaramar hukumar Bama ta jihar.
Majiyoyin sirri sun gaya wa Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa dakarun sojojin sun lalata maɓoyar ƴan ta'addan a wurare biyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sojojin sun fatattaki ƴan ta'addan ne a Bula Shetan, Lawanti, Garin Ari Shira, Kashimri da Gaizuwa.
Majiyiyoyin sun bayyana cewa dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda biyar a Garin Ari Shira tare da ƙona gaba ɗaya ƙauyen bayan sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan.
Haka kuma dakarun sojojin sun wuce zuwa Alafa. Amma bayan ƴan ta'addan sun ji ƙarar bindigu sun fice domin guduwa daga gidajensu.
Ƴan ta'addan sun yi wa sojojin kwanton ɓauna
A yayin da sojojin ke kan hanyarsu ta dawowa, ƴan ta'addan Boko Haram sun shirya musu kwanton ɓauna a Lawanti inda suka buɗe musu wuta.
Sai dai, sojojin sun yi nasarar daƙile harin tare da halaka ɗaya daga cikin ƴan ta'addan.
An samu bama-bamai da kekuna da sauran kayayyaki a hannun ƴan ta'addan da aka halaka.
'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Halaka Masunta a Borno
A wani labarin kuma, ƴan ta'addan Boko Haram sun halaka masunta masu yawa a wani mummunan hari a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kuma sace wasu masuntan masu yawa bayan sun zarge su da zama ƴan leƙen asirin jami'an tsaro.
Asali: Legit.ng