Kano: Kasurgumin Dan Daba Da 'Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Wuya Ga Hukumar

Kano: Kasurgumin Dan Daba Da 'Yan Sanda Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Mika Wuya Ga Hukumar

  • Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da cewa kasurgumin dan daba da ake nema, Chile Mai Doki ya mika wuya
  • Chile na daga cikin ‘yan daba uku da hukumar ta ayyana ta ke nema ruwa a jallo da ba da kyautar N100,000 ga duk wanda ya taimaka
  • Kakakin rundunar a jihar, Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar 5 ga watan Agusta a birnin Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano – Kasurgumin dan daba da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo a Kano mai suna Nasiru Abdullahi da aka fi sani da Chile Mai Doki ya mika wuya ga hukumar.

A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sanda a jihar ta sanar da sunayen ‘yan daba uku da take nema ruwa a jallo tare da ba da kyautar N300,000 ga duk wanda ya kawo su.

Kara karanta wannan

Kudi alaji: Yadda wani dan Najeriya ya dura wurin daurin aure da jaka makare da kudi ya girgiza intanet

Dan daba da ake nema ruwa a jallo ya mika wuya a Kano
Rundunar 'Yan Sanda A Kano Ta Tabbatar Da Karbar Kasurgumin Dan Daba Da Ya Mika Wuya. Hoto: Vanguard.
Asali: Facebook

Sauran ‘yan daban biyu da ake nema sun hada da Hantar Daba da ke Kwanar Disu da Abba Barakata na Unguwar Dorayi.

Dan daban ya mika kansa tare da neman afuwar hukumar

Mai Doki ya mika kansa a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai a ranar Asabar 5 ga watan Agusta inda ya ce ya dade ya na kwana a makabartu don gudun kamun ‘yan sanda, Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya tabbatar da cewa sun karbi tubabbun ‘yan daba da suka mika wuya fiye da dari, cewar Aminiya.

Kiyawa ya ce Mai Doki ya bukaci rundunar da su yi masa afuwa inda ya ce ya tuba da aikata muggan laifuka yayin da ya yi alkawarin taimakawa rundunar wurin kawo zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

Kiyawa ya gargadi mutane kan tsangwamar dan daban

Daga bisani, Kiyawa ya ja hankalin mutane da su kiyayi tsangwamar Mai Doki don samun shiryuwarsa gaba daya.

Ya ce:

“Har yanzu akwai kyautar kudi N100,000 ga duk wanda ya kawo sauran ‘yan daba biyu da ake nema ruwa a jallo.
“Idan mutum ya na da masaniya ko bayani a kan wadannan ‘yan daba, ya hanzarta zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da shi.”

'Yan Sandan Kano Za Su Ba Da Kyautar Kudi Ga Wanda Ya Kawo Bayani Kan Wasu 'Yan Daba 3

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a Kano ta ba da kyautar kudi N100,000 ga wanda ya kawo bayanai a kan wasu 'yan daba.

Hukumar ta ce ta na neman 'yan daban uku ruwa a jallo da suka hada da Chile mai Doki da Hantar Daba da kuma Barakata.

Rundunar ta ce duk wanda ya kawo su uku ya na da kyautar kudi N300,000 daga aljihun kwamishinan 'yan sanda a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.